✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bawa ya gyagije ya koma bakin aiki, inji EFCC

EFCC ta ce Mista Bawa yana cikin koshin lafiya, yar ya koma bakin aiki

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta ce shugabanta, Abdulrasheed Bawa, yana cikin koshin lafiya bayan ya yanke jiki ya fadi.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, a cikin wata gajerurwar sanarwa, ya ce tuni aka ba wa shugaban hukumar kulawa kuma har ya koma bakin aiki.

“Wannan bayani yana da muhimmanci saboda abin da ya faru ranar 16 ga Satumba, 2021 a Fadar Shugaban Kasa a lokacin da yake jawabi, ya samu matsalar da ta sa ya koma kan kujerarsa; Tuni aka ba shi kulawa har ya koma bakin aiki,” inji sanarwar.

  1. – Yadda shugaban EFCC ya sume a wurin taro

Aminiya ta kawo rahoton yadda Mista Bawa ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake jawabi a taron Ranar Karbar Katin Shaidan Dan Kasa da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa.

Bawa na taka bayani a taron sai aka ji ya yi shiru, a daidai gabar da yake magana kan wani matashi da EFCC ta kama a Jihar Oyo dauke da layukan waya guda 116.

Daga nan sai shugaban na EFCC ya budi baki ya ce, “Don Allah a yi min hakuri, ba zan iya ci gaba ba.”

A nan ne Ministan Sadarwa, Dokta Isa Ali Pantami tare da wasu manayan baki suka yi sauri suka taso suka rike shi.

Ana cikin haka ne Bawa mai shekara 41 ya yanke jiki, nan take aka fice da shi daga Fadar Shugaban Kasar.