✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci: UNICEF ta bukaci soke hukuncin kotun Musulunci

UNICEF ta ce kuskure ne hukuncin da aka yanke wa wanda ya yi batanci ga Allah a Kano

Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta Tarayya da su soke hukuncin da Kotun Musuluncin Jihar ta yanke wa wanda ya yi batanci ga Allah a Jihar.

UNICEF ya ce babu adalci a daurin shekara 10 da aiki mara wahala da kotun ta yanke wa Omar Farouq saboda munanan kalaman da ya furta ga Allah.

Wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins, ya ce, “Yanke wa yaron – Omar Farouk mai shekara 13 – hukuncin daurin shekara 10 a kurkuku da aiki mara wahala kuskure ne.

“Hukuncin ya saba wa ginshikan kare hakkin yara da yi musu adalci da Najeriya – da ma Jihar Kano — ta sanya wa hannu”.

Don haka ya yi kira da a “hanzarta amincewa da Kudurin Dokar Kare Yara ta Jihar Kano domin tabbatar da cewa dukkannin yara ’yan kasa da shekara 18, har da Omar Farouq da sauran yara a Kano sun samu kulawa daidai da tsarin kare hakkin yara”.

A ranar 4 ga watan Maris ce Omar Farouq ya yi mummunar furuci ga Allah a lokacin wata zazzafar muhawa.

Bayan saurayin a kashin kansa ya yi ikirarin aikata laifin ne alkalin Kotun Shari’ar Musuluncin, Khadi Muhammad Ali-Kani ya yanke masa hukuncin dauri daurin shekara 10 da aiki mara wahala.

Alkalin ya ce laifin ya saba wa Sashe na 382 (b) na Kudin Penal Code na Jihar Kano (2000) sannan ya ba wa wanda ake tuhumar damar daukaka kara cikin kwana 30.

Ya saba yarjejeniyar kasashe —UNICEF

Amma a martaninsa ga hukuncin, jami’in na UNICEF ya ce hukuncin “Ya saba yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na Kare Hakkin Yara Kanana da Najeriya ta sanya hannu a kai a 1991.

“Ya kuma ci karo da Yarjejeniyar Afirka ta Kare Yara da Walwalarsu – da Najeriya ta sanya wa hannu a 2001 – da Dokar Hakkin Yara ta Najeriya ta 2003, wadda kasar ta yi domin tabbatar wa kasashen duniya alkawarinta na kare rayuka da cigaban kananan yara”, inji Hawkins.

Ya ce asususun zai ci gaba da taimaka wa Gwamnatin Najeriya da ta Jihar Kano wurin kare hakkin yara da sauye-sauye a bangaren shari’a domin ganin jihohi sun dauki matakai da suka dace a kan batutuwan da suka shafi yara.