✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: Salman Rushdie ya zama mai ido daya

Hannun Salman Rushdie, marubucin da yi batanci ga Manzon Allah (SAW) ya daina aiki

Mutumin nan da aka kai wa hari bayan ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW), Salman Rushdie, ya makance a ido daya sannan hannunsa daya ya daina aiki.

Andrew Wylie, wanda ke wakiltar manyan marubuta irin su Saul Bellow da Roberto Bolano, ya bayyana wa jaridar El Pais ta kasar Andalus cewa idon Salman Rushdie daya ya daina gani kuma ya samu munanan raunuka.

“Ya samu munanan raunuka uku a wuyansa, hannunsa daya kuma ya daina aiki saboda jijiyoyin hannun sun tsinke, sannan akwai karin yanka sama da 15 a kirjinsa da wasu sassan jikina.”

Willie ya kara da cewa, raunukan da marubucin ya samu a harin da aka kai masa da wuka na iya halaka shi.

Sai dai ya ki bayyana ko an sallamo murubucin mai shekara 75 daga asibiti, da wata biyu bayan ’yan sanda sun tsare matashi mai shekara 24 da ya caccaka masa wuka a lokacin da yake gabatar da lacca.

Hannun nasa da idonsa daya sun daina aiki ne bayan harin wuka da wani matashi mai shekara 24 ya kai masa a lokacin da yake jawabi a kan mumbari, a wani taron adabi a birnin New York na kasar Amurka a watan Agustan 2022.

Bayan harin ne aka kai shi zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar ya samu raunuka a hantarsa, wasu jijiyoyinsa sun tsinke, sannan akwai yiwuwar ya rasa idonsa da kuma hannunsa daya.

Marubucin ya gamu da wannan mummunar akiba ne shekara 33 bayan Jagoran Musulunci na kasar Iran, Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya ba da umarnin kashe shi.

Ayatolla ya ba da umarnin ne watanni kadan bayan Rushdie ya wallafa wani littafi da ya sanya wa suna ‘Ayoyin Shaidan’ wanda a ciki ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW).

Marubucin ya shafe shekara tara yana buya karkashin kulawar ’yan sanda a kasar Birtaniya, bayan an sanar da tukwici mai tsoka ga dun wanda ya aika shi lahira.