Femi Falana ya kai karar gwamnatin jihar Kano da ta Tarayya a gaban Hukumar Kare Hakkin Bil-Adama ta Afrika da ke Banjul, babban birnin kasar Gambia, game da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mawaki.
Da ma dai Mista Falana, wanda babban lauya ne kuma mai rajin kare hakkin bil-Adama, ya daukaka kara don kalubalantar hukuncin da aka yanke wa Sharif Yahaya Sharif, matashin da aka tuhuma da laifin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a Kano.
- Ina so a rika yanke wa masu fyade hukuncin kisa – Ministar Buhari
- Mutum 18 sun kone kurmus a hatsarin mota
A sakon da ya aika mai dauke da kwanan watan ranar 8 ga watan Satumba, Mista Falana ya nemi hukumar da ta shiga lamarin, saboda a cewarsa an danne wa matashin hakkinsa yayin da ake neman zartar masa da hukuncin kisa.
“Na rubuto muku wannan sako a madadin Sharif Yahaya Sharif don neman Hukumar ta yi la’akari da wannan bukata cikin gaggawa.
“Na gabatar muku da bukatar ne tare da isar da sako a madadin Sharif Yahaya Sharif wanda aka yanke masa hukuncin kisa saboda aikata sabo a jihar Kano ta Najeriya”, inji shi.
Fitaccen lauyan ya ce duk da an daukaka kara, muddin hukumar ba ta yi gaggawar shiga lamarin ba, to kuwa babu tabbacin za a yi wa matashin adalci domin babu wata alama da ke nuna za a fasa zartar da wannan hukunci.