✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi

"Na san wanda aka kashen don na ma taba taimaka masa"

Matasa a garin Sade da ke Karamar Hukumar Darazo ta Jihar Bauchi, sun kashe wani matashi sannan suka kona gawarsa kurmus kan zargin sa da yin batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Mutanen da dama da suka zanta da Aminiya ta wayar tarho a garin Sade sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Wani tsohon babban jami’in gwamnati da ya fito daga garin na Sade da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “Na san wanda aka kashen don na ma taba taimaka masa, na kuma samu labarin abin da ya faru duk da cewa na yi tafiya yanzu.”

“An zarges hi da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) kuma har an kai karar shi a yayin da sakacin ’yan sanda ya sa har matasa suka far masa suka kashe shi.”

Neman jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Ahmed Wakili ya ci tura.

Bai amsa kiran wayar da Aminiya ta yi masa ba ko rubutaccen sakon da ake aike masa.

Sai dai wani jami’in dan sanda na Rundunar ya tabbatar wa da wakilin Aminiya cewa an kashe wannan matashi an kuma kona gawarsa.