Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Murtala Usman Mani ya ce ’yan sanda sun samu nasarar kama batagari da ake zargi da aikata miyagun ayyuka da suka hada da yin garkuwa da mutane a sassan jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne lokacin da ya gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai a ranar Larabar makon jiya.
Kwamishinan ya ce a ranar 30 ga Maris da ya gabata, wani mai suna Usman Ibrahim da ke kauyen Kaida a karamar Hukumar Isah ya kai kuka ga ’yan sanda cewa wani ya kira shi a waya ya yi masa barazanar ya kai kudi ko su sace ’yan uwansa. Ya ce binciken da ’yan sanda suka yi ya gano mutum biyu ne suka kitsa hakan kuma sun karbi Naira dubu 120 daga hannunsa kafin a kama su da ragowar Naira dubu 100 da 900.
Wadanda ake zargin, Sa’idu Ali da Ibrahim Mainasara suna zaune ne a kauyen Kaida, kuma Mainasara ya shaida wa Aminiya a inda suke tsare cewa, “Wannan lamari kaddara ce shi ne na farko kuma na karshe kuma tsora ta shi na yi kuma sai ya kawo kudin na amsa.”
Shi kuma Sa’idu ya ce shi ya ba da lambar wayar mutumin ga abokinsa don ya kira shi ya ba shi tsoro. “Haka kuma aka yi, mutumin ya tafi kauyensu ya kai masa kudin daga baya ya kawo min Naira dubu 40 ya dauki dubu 80. kaddara ce ta sanya ni hakan, ni da ke zuwa daji in saro itace in ciyar da iyalina mace biyu da ’ya’ya tara amma na fada cikin wannan, na yi nadama ba zan kara ba,” inji shi.
Kuma an kama wani matashi mai yin jabun Dalar Amurka mai suna Yahaya Isah tare da Dala 400 da daurin takardun yin jabun kudin da sauran wadanda ake zargi da laifuffuka daban-daban.