✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa sun bindige dan banga a garin Abba

An bindige matashin a garin Aba na Jihar Imo.

Wani matashi ya bakunci lahira bayan ’yan bindga sun bude mishi wuta a garin Abba da ke Karamar Hukumar Nwangele ta Jihar Imo. 

Matashin, mai suna Fidelis Nnadi, ya rasu ne bayan ’yan bindigar sun sun bude mishi wuta kan titin Okwelle zuwa Umuezealaibe da ke garin a ranar Laraba.

’Yan banga sun kashe hakimi da dan uwansa a Neja

Wata majiya ta ce “Na yi magana da wani kwamandan tsaro a yankin wanda ya shaida min cewa Fidelis ya je Okwele ne yin cefane, a hanyarsa ta dawo ce hakan ta ritsa da shi.

“Masu garkuwa da mutanen sun harbe shi ne a lokacin da suka tunkari garin Okigwe a cikin mota,” inji shi.

Mutumin da aka kashe dan banga ne kuma an kashe shi bayan ya baro kauyensu na Ogwuaga zai je Okwelle domin yin cefane, an hanyarsa ta dawowa ne gungun wasu ’yan bindiga suka bude mishi wuta.

’Yan bindigar sun bude mishi wuta ne bayan sun yi arba da shi, a yayin da suke kokarin tafiya da wata mata da danta da suka yi garkuwa da su.

Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya ce sun fara gudanar da bincike a kai.