A ranar Laraba ce a ka wayi gari da sanarwar rasuwar Muhammad Sunusi Barkindo, Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC mai shirin barin gado.
Ya rasu ne wajen misalin karfe 11:00 na daren Talata, ‘yan sa’o’i bayan ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
- An sake damke fursunoni 551 da suka tsere daga kurkukun Kuje
- Kwankwaso ne Silar Talaucin ’Yan Najeriya 100m —Peter Obi
Ya rasu yana da shekara 63 a duniya.
Aminiya ta zakulo muku wasu abubuwa guda biyar dangane da marigayin da za a dade ana tunawa da shi.
- Shugabanci a kungiyar OPEC
Marigayin shi ne Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur – OPEC mai barin gado, kuma na hudu a jerin shugabannin da suka rike wannan mukami daga Najeriya.
- Wa’adin shugabancinsa
Shekarar marigayi Barkindo shida yana rike da wannan mukami kuma wa’adinsa na Shugabanci zai kare ne a watan Agusta na shekarar 2022.
- Fafardo da farashin danyen mai a kasuwar duniya
Daya daga cikin nasarorin da marigayin ya samu a lokacin shugabancina shi ne farfado da darajar danyen mai a kasuwar duniya bayan da farshin ya fadi zuwa kasa da Dala 10 kan kowacce ganga sakamakon samar da wata yarjejeniya ta hadin kai da kasashen da ke ciki da kuma wajen kungiyar.
- Ganawa da Buhari a daren da zai rasu
Marigayi Barkindo ya rasu ne a daren Talata a Abuja, wasu sa’o’i bayan ganarwarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
- Sarautar Walin Adamawa
Marigayi Muhammad Barkindo har zuwa lokacin rasuwarsa shi ne yake rike da sarautar Wali Fombina na Adamawa.
Marigayin ya rasu yana da shekara 63 da haihuwa, ya kuma bar mata biyu da da daya.