✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona za ta halarci gasar cin kofin yashi a Legas

Kulob din Barcelona da ke Sifen zai kawo ziyara Legas don fafatawa a gasar cin kwallon kafa na yashi  da ake wa lakabi da (2014…

Kulob din Barcelona da ke Sifen zai kawo ziyara Legas don fafatawa a gasar cin kwallon kafa na yashi  da ake wa lakabi da (2014 Copa Lagos Beach Soccer Tournament) wanda zai gudana a tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Disamban wannan shekara.
Kamfanin da ya jagoranci daukar nauyin gasar mai suna Kinetic Sports ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta wuce a Legas.  Kamfanin ya ce baya ga kulob din Barcelona da ke Sifen, sun samu tabbacin kulob din Stationery Stores na Legas ma zai fafata a gasar.
Sauran kasashen da ake sa ran za su halarci gasar sun hada da Suwizilan da Kwaddebuwa da kuma kasa daya da har yanzu ba a tantance ba.  Sannan kungiyar kwallon kafa ta kasa mai rike da kambun ita ma za a fafata da ita.
Najeriya ce ke rike da kambun gasar kuma wannan shi ne karo na hudu da gasar ke gudana a Legas.  
Kamfanonin da ake sa ran za su dauki nauyin gasar a matsayin hadin gwiwa sun hada da na 1960 Bet da kuma Bankin FCMB.
Ana gudanar da gasar ce a duk shekara a Legas kuma wannan shi ne karo na hudu da aka fara gasar a Najeriya.