Kungiyar Barcelona ta sayi dan wasan gaba na Manchester City da kasar Sifaniya, Ferran Torres mai shekaru 21.
Sanarwar da Barcelona ta fitar a yammacin Talata ta ce a ranar Litinin mai zuwa 3 ga watan Janairu, za ta gabatar da sabon dan wasan da ta yi cefanensa Manchester City.
- Yadda mata da ’ya’yan mazan da ke zuwa ci-rani ke shiga kunci
- Fetur din da ke Neja Delta na ’yan Najeriya ne baki daya —Obasanjo
Masana tamaule na ganin cewa a halin yanzu Torres shi ne dan wasa mafi muhimmanci da Barcelona ta kulla yarjejeniya da shi, tun bayan rabuwa da gwarzonta Lionel Messi, wanda a yanzu yake taka leda a PSG da ke gasar Ligue 1 a Faransa.
Bayanai sun ce an dai cimma matsaya tsakanin City da Barcelona kan sauyin shekar Torres a kan euro miliyan 55, kudaden da wasu majiyoyi suka ce Barcelonan ta samu ne ta hanyar karbar bashi daga banki, la’akari da matsin tattalin arzkikin da take ciki.
Bayan komawarsa Manchester City daga Valencia, Ferran Torres ya ci kwallaye 16 daga cikin wasanni 43 da ya bugawa kungiyar ta City a ciki da wajen gasar Firimiya, inda ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofin gasar, da kuma kofin Carabao.