✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona ta dauki Aguero daga Manchester City

Aguero ya shafe tsawon shekara 10 yana murza leda a Manchester City.

Dan wasan gaban kungiyar Manchester City, Sergio Kun Aguero, ya koma Barcelona inda zai ci gaba da taka leda a kakar wasanni mai zuwa.

Dan wasan na Kasar Argentina ya rattaba hannu kan yarjeneniyar zama a kungiyar na shekara biyu bayan gwajin tabbatar da koshin lafiyarsa da aka gudanar ranar Litinin a Camp Nou.

Kungiyar Barcelona ce ta tabbatar da hakan cikin sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin.

A sakon da Barcelona ta wallafa ta rubuta sunan Aguero tare da wallafa hotonsa sanye da rigar kungiyar.

Aguero mai shekara 32 wanda ya shafe tsawon shekara 10 yana murza leda a Manchester City ya koma Barcelona ne kyauta.

Barcelona ta yi zawarcin dan wasan ne bayan da kwantaraginsa a Manchester City ya kare kuma ya yanke shawarar ba zai sabunta yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar ba.