✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barazanar ‘Yan Ta’adda: An Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja

Babban Sufetto ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya bayar da umarni da a tsaurara matakan tsaro a Abuja domin kare babban birnin daga barazanar ’yan…

Babban Sufetto ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya bayar da umarni da a tsaurara matakan tsaro a Abuja domin kare babban birnin daga barazanar ’yan ta’adda.

Sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan, Olumiyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata, ta ce rundunar ba za ta gajiya ba wajen kare babban birnin daga duk wata barazana.

Babban Sufeton ya bayar umarnin da a karo ’yan sanda domin kare wasu muhimman wurare da kadarorin gwamnati.

Ya kuma umarci bangaren tattara bayanan sirri na rundunar, da ya kara yawan jami’ai, da hanyoyin tattatara bayanai, da kuma rarraba shi ga sauran hukumomin tsaro don samar da kariya.

Usman Baba ya kuma yi kira ga mazauna Abuja da kewaye da su, “Hada kai da rundunar ’yan sanda da kuma sauran hukumomin tsaro ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen dakile afkuwar wani mummunan al’amari a birnin”.

Daukar wadannan matakai na zuwa ne bayan mazauna Abuja sun shiga zaman dar-dar sakamakon wasu bayanan sirri da aka kwarmata da ke nuna ’yan bindiga na shirin far wa garin na Abuja.