✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barazanar da takarar Atiku ke fuskanta a PDP

Ba zan taba goyon bayan makiyin al’ummar Binuwai ba.

Wata uku kafin gudanar da babban zaben da ke tafi, ga alama babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta gaza fita daga rikicin da take ciki, sakamakon rashin hadin kai a tsakanin mambobinta.

Takaddamar da ake samu a wannan lokaci tsakanin ’ya’yan jam’iyyar ta samo asali ne bayan zaben da Atiku Abubakar ya yi wa Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa a takarar.

Tun wancan lokaci rigingimu suka rika kunno kai musamman a tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike da bangaren Atiku Abubakar.

Yadda matsalar ta taso

Zaben Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin dan takarar mataimaki da Atiku Abubakar ya yi shi ne musababbin matsalolin da PDP ke fama da su a yanzu.

Sai kuma batun Shugaban Jam’iyyar PDP, Mista Iyorchia Ayu da ke fuskantar adawa, inda bangaren Wike ke matsa masa lamba cewa lallai ya sauka.

A baya-bayan nan bangaren Wike ya kafa kungiyar gwamnoni biyar da suke yi wa kansu lakabi da G-5.

Wadannan gwamnonni sun hada da na Jihar Ribas da Oyo da Abiya da Benuwai da Enugu, inda suka yi ikirarin cewa sun hada kansu ne don ceto kasar nan.

Girman barazanar

Duk da cewa har yanzu bangaren Atiku na ganin yana da karfi kuma ba lallai ne wannan barazana ta yi tasiri ko kawo masa nakasu ba, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai matsala babba.

Gwamnan Jihar Benuwai, Mista Samuel Ortom ya ce, za su ci gaba da zama a PDP su biyar din, sai dai ba za su mara wa Atiku baya ba.

Gwamna Ortom ya ce, ba za su goyi bayan mutumin da bai damu da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankunansu ba.

Gwamnan ya ce, sun gana da Wike na Ribas da Makinde na Oyo da Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu a Landan don cim ma yarjejeniya a tsakaninsu.

Gwamnan wanda shi kansa ke ganin Atiku ya yi rashin adalci ga Wike, ya ce shi da abokansa gwamnonin na neman lallai dan takararsu Atiku ya yi sulhu da Wike.

Wadannan gwamnoni biyar na ganin dole ne a yi wannan tafiya da su muddin ana neman kaiwa ga nasara.

Sai dai rikicin PDP ba wai kawai a nan ya tsaya ba, domin a Bauchi ma Atiku na fuskatar babban kalubale ganin Gwamnan Jihar na nuna masa yatsa bayan da ya zargi Atikun da yi masa zagon kasa kan batun sake zabensa a Gwamna.

Shugabannin Jam’iyyar PDP a jihar sun zargi wasu fitattun ’ya’yan jihar da shisshige wa Atiku Abubakar, duk da yake a can kasa ba sa cikin PDP.

A wata wasika da shugabannin PDP suka aike wa uwar jam’iyyar ta kasa, sun ja hankalin dan takarar cewa, ya kwana da sanin cewa wadanda yake ja a jika daga Jihar Bauchi ’yan zagon kasa ne kawai.

Ko akwai mafita?

Masanin Siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano, a tattatnawa da BBC, ya ce, ya kamata tun farko a yi tattaunawar siyasa domin warware matsalar.

Farfesa Kamilu ya ce, a yanzu gaskiya wannan yanayi babbar illa ce ga PDP, saboda cikin wadannan gwamnoni biyar akwai daga Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da duk wanda ya rasa su, to zai yi wahala ya samu iya cim ma kasar nan baki daya.

Sannan ya ce, babu mamaki dama na ciki na ciki, musamman a bangaren Wike da ya nuna burin takara ya kuma kashe makudan kudi.

“Sauran watakila su ma akwai wata jikakkiya a tsakaninsu da Atiku. Babbar matsalar ita ce dukkansu sun gaza nuna kwarewarsu ta siyasa, wajen shawo kan matsalolinsu a tafi tare.

“Yanzu kowa gani yake shi sarki ne, ga kuma batun masu zuga su daga gefe. Idan PDP ta ci gaba da tafiya a haka, to za ta yi babbar asara a zabe mai zuwa,” in ji Farfesan.

Farfesa Kamilu ya kuma ce, a tsarin dimokuradiyya ko mutum guda ka rasa asarar ce, yanzu ga shi Bauchi ma na rawa.

A siyasar Najeriya gwamnoni na da muhimmanci sosai da karfi a jihohinsu. Don haka, idan har Atiku bai dinke barakar PDP ba kafin zabe, tafiyar ta kasance guda, to zai yi wuya ya kai labari.

Masana dai a yanzu na ganin shawara ta rage ga mai shiga rijiya, domin a yanayin da abubuwa ke tafiya a PDP sulhu ne kawai abin da zai iya ceto ta a wannan lokaci.

Bazan taba goyon bayan Atiku ba —Ortom

Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya ce, babu shi babu dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Gwamna Ortom ya ce, Atiku ya yi duk abin da ya ga dama, amma babu ruwansa da yakin neman zabensa.

“Atiku da masu goyon bayansa su yi duk abin da suka ga dama, amma da in goyi bayansa ya zama Shugaban Kasa gwanda in mutu.

“Ba zan taba goyon bayan makiyin al’ummar Binuwai ba,” in ji Gwamnan.

Ba a fahimce ni ba —Ortom

A ganawar da suka da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Samuel Otom ya yi amfani da damar wajen ba da hakuri ga kalaman da ya furta cewa sam ba zai zabi Bafulatani a matsayin shugaba ba, da cewa gara ma ya mutu da ya goyi bayan Bafulatani.

Otom na ganawa da tawagar gwamnoni biyar ne da su ka yi wa jam’iyyar PDP bara’a kan Shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga mulki don shugabancin ya koma Kudu.

Gwamna Otom wanda dama ya saba furta irin wadannan kalamai na kabilanci, ya ce ya san ko yaya, za a yi ma sa fassarar da ba lalle haka ya ke nufi ba, don haka ya na ba da hakuri.

Ana iya tuna cewa, Otom a taron kaddamar da kamfen a Makurdi gaban gwamnonin PDP na bara’a, ya ce duk wanda ya mara wa Atiku baya makiyin Jihar Binuwai ne kuma shi sam ba zai zabi Bafulatani ba don zargin da ya ke yi cewa Fulani ke kashe al’ummar jiharsa.

Otom ya ce zai juyo kan ‘yan Majalisar Dokokin Tarayya da ke hada kai da Shugaba Buhari wajen zubar da jinin mutanen Binuwai.

“Da in zama bawan Fulani gara na mutu ma,” inji Otom.

Gwamnonin G5 sun ziyarci Jihar Binuwai, kafin taron kaddamar da yakin neman zabe na jam’iyyar da nufin kaddamar da ayyukan da gwamnantin Ortom ta kammala.

Kungiyar da Wike ke jagoranta tana adawa ce da tsarin Jami’iyyar PDP ke kai na samar da dan takarar Shugaban Kasa daga Arewa, sannan kuma a ce Shugaban Jam’iyyar ta Kasa Iyorchia Ayu ya fito daga yankin.