✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barayi sun fasa gidan Benzema lokacin da Madrid ke wasa

Barayin sun shiga gidan dan wasan lokacin da babu kowa a ciki.

Wasu barayi a ranar Lahadin sun shiga gidan dan wasan gaban Real Madrid, Kareem Benzema, yayin da kungiyar tasa ke buga wasa da Elche.

Wannan shi ne karo na biyu da barayi ke shiga gidan dan wasan a lokacin da ba ya cikin gidan.

Ko a watan Fabrairun 2019, yayin da Real Madrid da Barcelona ke fafatawa, barayi sun shiga gidansa lokacin babu kowa a ciki.

Sai dai ya zuwa yanzu, hukumomin tsaron birnin Madrid ba su fitar da sanarwar abin da aka sata a gidan dan wasan ba.

Lamarin fasa gida ko shiga gidajen ’yan kwallo da nufin yin sata ba sabon abu bane a kasar Spain.

’Yan wasan kungiyoyi daban-daban kamar su Casemiro, Carvajal, Antone Griezmaan, Thomas Lemar, Jao Felix, Luis Suarez, Bojar Mayoral da sauransu duk an shigar musu gida da nufin sata.

Benzema ya zubar da damar saka kwallo a bugun fenareti da Madrid ta samu a wasan nata da Elche, kafin dan wasan ya ji rauni a minti na 58.