Wani mutum ya gamu da ajalinsa a cikin tiransufoma a yayin da yake ƙoƙarin satar kayan wutar lantarki a Jihar Yobe.
Mutumin na ƙoƙarin sace kayan lantarkin daga wata tiransufoma ne ya gamu da ajalinsa a kan wani turken lantarki a rukunin gidajen kwamishinoni da ke garin Damaturu.
Ana zargin barawon ya hau turken da ke dauke da tiransufoma ba tare da sanin cewa an dawo da wutar ba, kasancewar da farko an dauke ta, to shine fa mai faruwa ta faru.
Blessing Tunoh, babbar, jami’ar sadarwa ta Kamfanin Rarraba Lantarki ta Yola (YEDC), ta bayyana cewa manajan yanki na kamfanin, ya ziyarci yankin, bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Blessing ta ce, ’yan sanda ne suka fitar da gawar wanda ake zargin zuwa Asibitin Koyarwa na Damaturu.
Kakakin kamfanin na YEDC ta ce da jin haka ’yan uwan mamacin suka zo suka tabbatar da gawar ɗan uwansu ne a lokacin da suka isa asibitin.
DSP Dungus Abdulkarim, kakakin ’yan sanda na Jihar Yobe, ya tabbatar da cewar, marigayin ya yi yunkurin sace kayan ne da misalin karfe 1:00 na dare yayin da hakan ta faru.
A cewarsa, “a lokacin an dauke wutar amma kwatsam sai wutar ta kama shi ya gamu da ajalinsa nan ta ke.
“Da asubahi ne mazauna rukunin gidajen suka gano gawarsa a kan hanyarsu ta zuwa masallaci domin yin Sallar Asuba.
“Za mu ci gaba da tallafa wa kamfanin YEDC wajen kare kadarori da kuma gurfanar da barayin da aka kama wadanda ke lalata kayan wutar lantarki.”