✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barawon kwamfuta ya aike wa mai ita sakon neman afuwa

Ban damu ka dawo min da kwamfutar ba, saboda na sa na’urar bibiya a jikinta.

A kasar Indiya, wani sakon Tuwita ya karade shafukan sada zumunta bayan da wani barawo ya nemi afuwar mutumin da ya sace wa kwamfuta ’yar yawo yana bayyana masa cewa rashin kudi ne ya sa ya yi masa satar.

Wanda aka yi wa satar ya sa hoton sakon da barawon ya rubuta masa ta adireshinsa na Imel bayan sace ta a shafin Tuwita.

Ya rubuta sakon Tuwita kamar haka: “Sun sace min kwamfuta jiya da dare, kuma sun aiko min sako ta Imel dina, na samu kaina a cikin takaici da kuma ban dariya a yanzu.”

Baya ga neman afuwa kan sace kwamfutar, barawon ya kuma hada da wani shirin gudanar da binciken karatu da yake tsammanin mai kwamfutar yana aiki a kai, inda ya tambaye shi ko yana bukatar wasu fayil-fayil da suka shafi aikin jami’a da suke cikin kwamfutar kafin ya sayar da ita.

“Na lura kana fama da wani binciken ilimi, na hado da shi, idan akwai wasu fayilfayil da kake bukata don Allah ka sanar da ne kafin ranar Litinin da karfe 12 domin tuni na samu wanda zai saya,” ya fadi a sakon Imel din.

“Ina matukar ba ka hakuri kan dauke mata kwamfuta, ina fama da talauci da tsananin bukatar kudi,” barawon ya rubuta a cikin wancan sakon Imel.

Ya kara da cewa: “Na bar maka wayarka da jakar kudinka saboda ina tsammanin suna dauke da ’yan wasu abubuwa.”

Sakon yana bayyana a kafar sada zumuntar sai mutane suka shiga tausaya, yayin da wasu suka rika nuna mamaki.

Sakon Tuwitar wanda aka buga a ranar Lahadin da ta gabata ya samu wadanda suka sake tura shi har mutum dubu 30, yayin da dubu 250 suka nuna sha’awa a kai.

Wasu masu sharhi sun nuna shakku a kan ingancin labarin. Kuma daya daga cikinsu ya nuna wani hoton irin wannan sako inda ya ce, mutumin ya kwafo ne kwabo da kwabo don kawai ya yi “suna.”

Daya daga cikin wadanda suka yi tsokaci a kan sakon ya rubuta cewa: “In da ni ne sai in ba shi amsa da cewa, “Ban damu ka dawo min da kwamfutar ba, saboda na sa na’urar bibiya a jikinta.

Don haka ’yan sanda za su gano ta ya alla a inda ka aiko wannan sako ko kuma wanda zai saya daga hannunka. Mu wuni lafiya.”

Bayanan baya-bayan nan sun ce yanzu haka mutumin yana kokarin ya sayi kwamfutar daga barawon.

%d bloggers like this: