Shahararren dan kwallon gaban kulob din Real Madrid da ke Sifen da ya canza sheka zuwa na Napoli da ke Italiya ya bayyana cewa bai yi nadamar barin kulob din ba ganin yadda kocin kulob din na yanzu Carlo Ancelloti ya rika nuna masa wadansu halayen da bai gamsu ba.
Gonzalo Higuain wanda ya zura kwallaye fiye da 100 ga kulob din Madrid a gasar La-Liga a tsawon shekara bakwai da ya yi, ya ce bai ji dadin yadda kocin ya koma da shi benchi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Ya ce rashin sanya shi buga wasa a kan kari ce ta sa ya yanke shawarar barin kulob din zuwa na Napoli a cinikin da ya kai Yuro miliyan 40.
“Akwai lokutan da na ji dadi a zaman da na yi a kulob din Madrid sannan akwai lokutan da ban ji dadin zama ba”, a hirar da ya yi da jaridar La Sedta a Ajantina.
Ban yi nadamar barin kulob din Madrid ba -Gonzalo Higuain
Shahararren dan kwallon gaban kulob din Real Madrid da ke Sifen da ya canza sheka zuwa na Napoli da ke Italiya ya bayyana cewa bai…