✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban san mutumin da ya maka ni a kotu kan maganar aure ba – Hadiza Gabon

Ta ce sam ba ta ma san mutumin ba

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta karyata batun mutumin da ya zarge ta da yaudararsa tare da cinye masa kudi Naira dubu 396 da cewa za ta aure shi.

A makon jiya ne mutumin ya kai kara kotu, inda ya zargi jarumar da cinye masa kudi sannan ta ki auransa.

Lauyan wadda ake karar, Barista Mubarak Sani Jibril ya ce, “Hadiza Gabon ba ta san mutumin ba, kuma ba su taba haduwa ba, ballantana ta masa alkawarin aure.”

Gabon ta bayyana hakan a zaman Kotun Shari’ar da ke Magajin Gari a Kaduna.

Da yake bayani, lauyan mai kara, Barista N. Murtala ya ce wanda yake wakilta din sun hadu da Hadiza Gabon ne a kafar Facebook, inda suka saba har maganar aure ta shiga.

“Bayan sun hadu a Facebook, sun shaku shi ne ta masa alkawarin aure, wanda hakan ya sa ya fara kashe mata kudi. Ta ce ba ta san shi ba, amma za mu kawo shaidu.

Alkalin kotun, Mai Shri’a Khadi Malam Rilwanu Kyaudai ya dage shari’ar zuwa 28 ga watan Yuni, sannan ya bayar da belin jarumar tare da bukatar ta kawo mutum biyu mazauna Kaduna da za su tsaya mata.