Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar PDP ne duk da cewa ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can.
A hirarsa da BBC, jagoran kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce a makonnin da suka gabata ne suka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna ‘The National Movement’, bayan nan ne aka samar da jam’iyyar NNPP wato New Nigeria People Party.
Kwankwaso ya ce, wannan sabuwar jam’iyya ce ta mutanen da suka amince cewa akwai bukatar tsarin da aka taho da shi daga shekarar 1999 a sauya shi a kawo abin da jama’a za su amfana.
Ya ce akwai bukatar nazari kan abin da kasa za ta sauya sannan ta samu sabon alkibla, sai dai yana mai jaddada cewa har yanzu ya na nan a cikin jam’iyyar PDP bai fita daga cikinta ba.
“A yanzu maganar da ake yi ina cikin jam’iyyar PDP, tun wancan lokacin mun fara abin hawa-hawa. Abu na farko da muka fara yi shi ne ja baya daga tsarin ta, tunanin wasu masu hankali za su zo a zauna a fada musu abin da ya dame mu amma jam’iyya ba ta yi ba, muka shiga kungiya nan ma ba a yi komai ba, to gamu a matakin jam’iyya.
“Har yanzu da na ke magana da kai muna tsakanin kungiya da jam’iyya sannan ban fita daga cikin jam’iyyar PDP ba, kuma wannan kungiya ta hade ne da jam’iyyar NNPP.
“Duk ranar da zan bar PDP ku ne na farko da za ku sani saboda abubuwan ne a tsare su ke mu na komai cikin tsanaki.”
Kwamkwaso ya ce ba wai ya raba kafa ba ne tsakanin jam’iyyar NNPP da PDP kuma idan manyan jam’iyyar PDP suka bukaci a sasanta tsakaninsu ya ce yanayin zai danganta da abin da suka fada da kuma yadda su sauran abokan tafiya suka kalli lamarin.
“Maganar ba ta Rabi’u Kwankwaso ko ta Kwankwasiyya ba ce, magana ce ta ‘The National Movement’ kuma muna da yawa a ciki, sannan yawancin wadanda ke cikin ta manyan mutane ne dan haka ba zan yanke hukunci ni kadai ba.”
Da aka tambaye tsohon gwamnan kan rahotanni da ke cewa an rushe shugabancin jam’iyyar NNPP tun ma kafin su shige ta da kuma kakkabe duk wanda ba dan Kwankwasiyya ba da yin sabon zubi da ‘yan Kwankwasiyya sai ya kada baki ya ce:
“A’a ai jam’iyyar daman ba ta mu ba ce, amma ana son mu zo a tafi tare don haka su na son mu kawo namu su ma su kawo nasu.
“Sannan lokacin shugabancinsu ya wuce don haka kowa ya sauka, ciki har da shugaban da ya yi mata rijista sama da shekara 20 da ta wuce.
“Don haka tsari ne ake hadawa da namu da nasu saboda mafi yawan jihohi ba su da kowa,” in ji Kwankwaso.