✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban bijire wa umarnin Osinbajo ba —Malami

Ministan ya ce shawara ya bayar a matsayinsa na nlauya ba Antoni-Janar ba.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya musanta zargin da ake masa da bijire wa umarnin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo a kan zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihohi.

A ranar 30 ga watan Yuli ne Osinbajo ya jagoranci wani taron manyan lauyoyi domin shawo kan matsalar rikicin da ya mamaye jam’iyyar, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zaben Gwamnan Jihar Ondo.

Bayanai sun ce Osinbajo ya jagoranci taron ne bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ba da umarnin a jingine gudanar da zabukan jam’iyyar a jihohi.

Sai dai Malami ya sanar da Aminiya cewa ba bijire wa umarnin  Mataimakin Shugaban Kasar ya yi ba, illa iyaka shawara ce ya bayar a matsayinsa na lauya cewa a gudanar da zabukan, ba a matsayin Atoni Janar din Najeriya ba.

Cikin wata takarda da mai magana da yawun Ministan, Umar Jibrilu Gwandu ya sanya wa hannu, Malami ya ce yadda za a tsara zabukan abu ne da ya shafi jam’iyyar APC kuma ba shi da alaka da kasancewarsa minista.

“Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa tsara yadda za a gudanar da zabe da taron jam’iyya duk alhaki ne na jam’iyyar siyasa ba na Ofishin Atoni Janar ba.

“Kuma kamar yadda aka sani, ba Malami ne kadai ke da alhakin tabbatar da an bi umarnin da ya shafi shugabancin jam’iyyar ba.

“Saboda haka hankali ba zai dauka ba idan aka ce Atoni Janar ya bijire wa wata doka da ba shi da ikon sauyawa a shari’ance,” inji Gwandu.