Babbar jam’iyyar adawa a Najeiya PDP, ta nemi a yi watsi tare da musanta zargin cewa ta dakatar da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiya, ta musanta wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta mai dauke da sakon dakatar da babban jigo a jam’iyyar.
PDP ta jaddada cewa, akwai wasu ka’idodi da kundin tsarin jam’iyyar suka tanadar gabanin dakatar da duk wani jigo daga cikin Majalisar Kusoshin jam’iyyar (NEC).
Da wannan ne jam’iyyar take gargadin cewa ba za ta lamunci irin wadannan karairayi ba da wasu masu neman kawo hargitsi ke yi da zummar haifar da rikici ko rabuwar kai a tsakanin mambobinta.
Kazalika, jam’iyyar ta ce ba ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Neja ba, Babangida Aliyu, inda take cewa duk bayanan da aka fitar na dakatar kusoshin jam’iyyar biyu basu da asali.
Jam’iyyar tana mai nuna bacin ranta kan irin wannan zantuka marasa asali, wanda a cewarta ka iya kawo zargi ko hargitsi a jam’iyyar.
Ta shawarci shugabanninta na Jihohin Kano da Neja da su hada kai wuri guda sannan su yaki irin wadannan bayanai na kanzon kurege da ka iya kawo rabuwar kai musamman a wannan lokaci da ’yan Najeriya ke matukar bukatar jam’iyyar.