Da yawa-yawan masu karatu sukan tambayi bambance-bambancen tsakanin cututtuka masu saurin yaduwa da marasa yaduwa a cikin al’umma. To a wannan mako za a duba bambance-bambance da ke tsakanin wadannan nau’ukan cututtuka biyu.Kuma dama saboda saukin fahimta kusan a yanzu an fi kasa cututtuka a likitance zuwa wadannan manyan rabe-rabe. Cututtukan gado da na daji a da akan ware su daban amma yanzu ilimi ya nusar da cewa da yawa-yawan cututtukan gado da na daji ma na iya shiga cikin wannan rabe-rabe, inda akan sa su a ajin cututtuka marasa yaduwa (duk da cewa za a iya yada su ta kwayoyin gado). Har ila yau akwai cututtuka masu yaduwa da za su iya sa ciwon daji. Don haka rabe-rabe kusan za su iya cukurkudewa idan ba a lura da kyau ba.
Abin da ake nufi da cututtuka masu saurin yaduwa su ne cututtukan da kwayoyin cuta kan samar. An halicci biliyoyin kwayoyin cuta masu iya sa mana cututtuka, watakila a same su a iska ko ruwa ko abinci ko ta hanyar taba mai ciwon ko ta hanyar cizon wata dabba ko kwaro. Wadannan cututtuka suna yaduwa idan wani ya dauka daga wani, misali idan wani ya yi tari ya watsa kwayoyin cututtukan a iska, wadansu da dama na iya kwasa, su ma ko su yi ciwo ko su ajiye a jikinsu su rika yadawa. Abin da kuma ake nufi da cututtuka marasa saurin yaduwa su ne cututtukan da sukan same mu haka kawai, saboda yanayin ci gaban zamani da halayya da zamantakewa da bambancin muhalli da ma gadon kwayoyin halittu a wasu lokuta. Misalan irin wadannan cututtuka su ne hawan jini da ciwon suga da ciwon asma da na zuciya.
Cututtuka masu saurin yaduwa, wasunsu kan iya shiga jikinmu su fita nan da nan bayan ’yan kwanaki ko watanni, idan aka sha musu magani, wasu kuma ko ma ba a sha ba, misalansu su ne kwayar cutar cizon sauro; wasu kuma idan suka shiga sun shiga ke nan mutu-ka-raba, misali kwayar cuta mai karya garkuwar jiki (kanjamau), wadda har yanzu ba a gano magani a likitance da zai kore ta daga jiki ba idan ta shiga. Su kuma cututtuka marasa yaduwa idan suka kama mutum, su ma kusan mutu-ka-raba, domin sai dai su tashi ko kuma su lafa amma da wuya a neme su a rasa.
Wani abin mamaki game da wannan rabe-raben cututtuka shi ne duk da cewa akwai biliyoyin kwayoyin cututtuka a duniya masu saka dubban cututtuka masu saurin yaduwa, cututtuka marasa saurin yaduwa a yanzu sun fi saurin kisa fiye da masu saurin yaduwa. Wannan kuwa ya faru ne saboda yadda zamani ya zo da zurfin bincike a kan magungunan waraka daga kwayoyin cutar, sabanin rashin magungunan waraka ga cututtuka marasa yaduwa. Wato zamani ya zo a yanzu kusan saboda magungunan da ake kerawa cututtuka masu saurin yaduwa ba sa kisa kamar yadda marasa saurin yaduwa ke yi. Domin an kiyasta yanzu a duniya gaba daya cututtuka marasa yaduwa su suka fi saurin kisa, don kuwa su ne musabbabin mutuwar kashi 70 cikin 100 na mace-mace da ake samu a duk shekara inji Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO). Wanda hakan na nufin cututtuka masu saurin yaduwa kusan su mace-macen da suke sa wa kashi 30 ne kadai.
Amma fa wannan lissafi kamar yadda muka fada, ci gaban zamani ne ya kawo haka, saboda yaduwar ilimin kiyaye aukuwar cututtuka masu yaduwa da bazuwar magungunansu a ko’ina a duniya. Idan mabiya tarihi ba su manta ba, a da cututtuka masu saurin yaduwa ne suka fi saurin kisa fiye da marasa yaduwa, domin a wancan zamani babu alluran rigakafi da magungunan kashe kwayoyin cuta, idan ciwo daya ya shigo gari sai ya yi sanadiyar rayukan kusan rabin mutanen garin ya kuma watsu a duniya. Misalan wadannan su ne annobar murar da aka yi a 1918 (shekara 100 cif ke nan da suka wuce) da wadda aka yi a kwanan nan a shekarar 2009. Annobar murar 1918 wadda ta faro daga kasar Spaini, ta yadu a sassan duniya har da Nahiyar Afirka, ta kama mutane fiye da miliyan 500, kuma ta jawo salwantar rayukan fiye da miliyan 100. Amma wadda aka yi ta shekarar 2009, wadda ta faro daga kasar Meziko ta bazu a duniya, fiye da mutum miliyan 200 ta kama amma ba ta kashe ko rubu’in miliyan ba. Wannan saboda ci gaban da aka samu na zamani ne kan hanyoyin kariya daga cututtuka da yaduwar alluran rigakafin mura a ko’ina. Sai dai ci gaban zamanin har ila yau ya haifar da yawaitar cutuka marasa yaduwa.