Tsohuwar Ministar Mata a Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2003, Hajiya Aishatu Isma’il, ta ce ilimin da suka samu tun daga matakin firamare har zuwa sakandare, ba shi da bamabamci da wanda aka bai wa daliban kasar Birtaniya na wancan lokacin.
Hajiya Aisha ta bayyana hakan ne a wata ganawa ta musamman da Aminiya, albarkacin Ranar Ilimin ’Ya’ya Mata ta Duniya ta 2022.
- ’Yan Kwankwasiya sun far min da wuka, sun kwace wayata —Hadimin Ganduje
- Buhari na neman ciyo bashin tiriliyan N11 a 2023
Ta ce sabanin ilimin yanzu, a da wanda ya kammala karatun sakandare zai iya fara aiki a ma’aikatu ko da bai samu wani horo ba daga baya.
Sai dai ta ce tabarbarewar ilimi ta sanya a yanzu ko wanda ya kammala jami’a ba za iya gudanar da aikin yadda ake so ba.
Bambamcin Ilimin ’ya’ya mata a da, da yanzu
Hajiya Aishatu ta ce kasancewar a da matan da ake sanyawa a makaranta ba su da yawa, lokacin da ta fara karatun firamare a garinsu, Gwarzo, shi ne aka taba samun dalibai mata 10 a aji daya.
“A lokacin ne aka samar da makarantun firamare na kwana, amma duk da haka ba a kaiwa mutane 25 a aji daya.
Tsohuwar ministar ta bayyana lalacewar ilimi a matakin firamare a matsayin tushen tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya a halin yanzu.
Fahimtar harkar mata ke kawo cigaban kasa
Ta ci gaba da cewa Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka (AU) da suaran kungiyoin duniya sun yi amannar duk kasar da ba ta fahimci harkar matan da ke cikinta ba, to ba za ta ci gaba ba.
“Duba, matsalar lafiya, ta mata ce, sannan dubi yadda Najeriya a yanzu ta fi kowacce kasa yawan masu mutuwa wajen haihuwa.
“To wadannan abubuwan ake dubawa idan aka tashi sabgar tattalin arzikin kasa,” in ji ta.
Ta ce haka lamarin yake a bangaren yara masu fama da yunwa da na ilimi, domin acewarta, idan yara ba su yi ilimi ba, matsalar matan yake komawa.
“Don haka lokacin da nake minista, kowacce ma’aikata ka je da teburinmu na mata da muke da mai aiki a wajen.
“Hatta bangaren noma muna da shi, domin idan kika duba, maza ne ke da noma, amma mata ne ke aikin a Najeriya da yankin Afirka baki daya.”
Aishatu Isma`il ta ce don haka dole ne a waiwayi matsayin mata harkar noma, don samar da tsare-tsaren kasa da za su yi daidai da su.