✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bama-bamai ba su isa su kawar da matsalar tsaro ba —Buhari Awwalu

ami'in ya ce bai wa shanin ilimin makiya muhimmanci shi ne mafita ga matsalar tsaro

An bayyana cewa, bama-bamai da alburusai ba za su iya kawar da matsalar tsaron da ke ci gaba da yi wa Najeriya barazana ba.

Daraktan Shiyya na Rediyon Tarayya na Najeriya (FRCN), Buhari Awwalu, shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce komai yawan bama-bamai da alburusan da za a yi amfani da su, ba za su magance kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta ba, musamman ma matsalar ’yan fashin daji.

Ya ce bai wa wadanda lamarin ya shafa, kamar makiya, nagartaccen ilimi ita ce hanya daya tilo da za ta taimaka wajen magance matsalar.

Ya kara da cewa rashin bai wa Fulani makiya muhimmanci, shi ne tushen matsalar ’yan fashin dajin da a yanzu ake fuskanta a kasa.

Buhari Awwalu ya yi wadannan bayanan ne a wajen taron ba da horo na yini biyar ga ma’aikatan Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya ta Kasa (NCNE) game da Shirin Rediyo a masatyin wani bangare na shirye-shiryen kaddamar da Rediyo Zamanu International, wanda aka kafa musamman domin ilimantar da makiyaya a fadin kasa a Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Buhari Awwalu, ta bakin Babban Manajan tashar Karama Rediyo Kaduna, AbdulRahman Nuhu Bayero, ya yi kira da a bai wa hukumar NCNE isassun kudade domin ba ta damar sauke nauyin da ya rataya a kanta yadda ya kamata.

Saboda, a cewarsa, “Ilimin makiyaya shi ne mabudin zaman lafiyar Najeriya. Muna bukatar shi don samun rayuwa mai armashi.

“Idan aka wadata hukumar da kayan aiki yadda ya kamata, ba za mu yi fama da matsalar tsaron da muke fuskanta a yau ba.

“Don haka, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya da hukumomin kasashen ketare su lalubo hanyoyin da za a bi wajen bai wa hukumar kulawar da ta dace don samun tsaro da zaman lafiyar kasa,” inji shi.

A nasa bangare, Sakataren NCNE, Farfesa Bashir Usman, wanda Darakata a hukumar, Mista Akin Akinyosoye ya wakilta, ya ce, “Abin a duba ne yadda ake samun yara marasa zuwa makaranta a Najeriya, musamman a tsakanin makiyaya, musamman kuma duba da yadda ake samun yawan rashin jituwa a tsakanin makiya da manoma.”

Daga nan, ya ce hukumar za ta yi amfani da sabuwar tashar Rediyon Zamanu International wajen yin kira da a zauna lafiya a tsakanin makiyaya da manoma, inda za su soma da a jihohin Gombe, Kano, Oyo da kuma Filato.