✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bala Mohammed ya lashe zaben fitar da gwanin PDP da aka sake a Bauchi

Gwamnan ya lashe kuri’un wakilai 646 da suka jefa kuri’a daga cikin 650.

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ya yi nasara a zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP da aka sake gudanarwa.

An sake zaben ne bayan Sakataren gwamnatin jihar da aka zaba tun da farko ya janye wa gwamna Bala Mohammed wanda ya fadi zaben fitar da gwani na Shugaban kasa.

Gwamnan ya lashe kuri’un wakilai 646 da suka jefa kuri’a daga cikin 650.

Cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar, Bala Mohammed ya ce, “Da farko ina mika godiyata ga babbar jam’iyyarmu ta PDP a Jihar Bauchi, da wakilanmu, da Sakataren Gwamnatin Jiha kuma tsohon dan takarar gwamna, Ibrahim Muhammad Kashim, wanda ya janye takararsa saboda karamci a gare ni.

Aminiya ta ruwaito cewa tun a makon da muke bankwana da shi ne jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi ta fara shirye-shiryen gudanar da sabon zaben fid-da-gwani na dan takarar Gwamnan Jihar.

Jam’iyyar PDP ta yanke shawarar sake zaben fid-dagwanin ne bayan da dan takarar jam’iyyar Alhaji Ibrahim Kashim Mohammed ya yi murabus.

Sakataren Labarai na Jam’iyyar PDP a Jihar, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya tabbatar da haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi Ya ce “Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Ibrahim Kashim ya janye takararsa don kashin kansa.

“Tunda ya sauka da kansa jam’iyyar ba ta da wani zabi illa ta samu wanda zai maye gurbinsa ta hanyar sabon zaben fid-da-gwani.”

Kashim ya yanke wannan shawara ce bayan da Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed ya gaza samun tikitin neman tikitin takarar Shugaban Kasa a PDP.

Alhaji Yayanuwa ya ce jam’iyyar na bin tsarin ne kamar yadda dokar jam’iyya da kuma dokokin zabe suka tanada, “Muna bin tsarin kuma za mu gudanar da sabon zaben fid-dagwani na Gwamna,” inji shi.

Ya ce “Gwamna Bala ya nemi tikitin takarar Shugaban Kasa ne bisa kiraye-kirayen da ’yan Najeriya daban-daban da masu kishin kasa suka yi masa, ya amsa kiran, a yanzu al’ummar Jihar Bauchi na son ya tsaya takara karo na biyu.

“Kuma duk abin da jama’a suka yanke shi ne za a yi, don Gwamna mutum ne mai sauraro, kuma mai amsa kiran al’ummarsa.”

Dama mutane da dama a Jihar Bauchi sun rika raderadin cewa Barista Kashim ya tsaya takarar ce don rika wa Gwamna Bala Mohammed wanda suke ganin da wuya ya kai bantensa a takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP.