✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bakanon da ke tattaki zuwa Legas saboda Tinubu ya isa Ibadan

Yana tattakin ne don nuna goyon bayansa ga takarar Tinubu a 2023

Wani Bakanon da ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas domin nuna goyon bayansa ga takarar Bola Tinubu, Husseini Lawal, ya isa Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Mutumin dan asalin Jihar Kano ya fara tattaki ne zuwa Legas tun bayan da Tinubu wanda jigo ne a jam’iyar APC mai mulki ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a kakar zabe mai zuwa.

Hussein ya isa birnin Ibadan a daren Litinin inda ya bayyana cewa yayin tattakin nasa yana samun tallafi na kudi da sauran abubuwa daga sojoji da direbobin da yake haduwa da su a kan hanyarsa.

Har ila yau, ya shaida wa wakilinmu cewa ya fara tattakin ne domin nuna cikakken goyon bayansa ga tsohon Gwamnan na Legas saboda ya ce shi kadai ne dan takarar da ya damu da matasa a cikin masu neman takarar a 2023.

“Tinubu ya goyi bayan matasa tun kafin ya zama Gwamna a Legas; haka kuma lokacin da yake Gwamnan da ma bayan ya bar kujerar,” inji mai tattakin.

Daga karshe ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mara wa Tinubun baya a zabe mai zuwa.