✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai wa ’yan bindiga kuɗin fansa na dagula sha’anin tsaro — Ribadu

Ya roƙi 'yan Najeriya da su daina bai wa 'yan bindiga kuɗin fansa a duk lokacin da suka sace wani nasu.

Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kuɗin fansa.

Ribadu, ya ce biyan kuɗin fansa ba ya sa ana sakin waɗanda aka sace, kuma hakan na ƙara dagula al’amuran tsaro.

Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, yayin da yake karɓar mutane 64 da dakarun tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da su a Zangon Kataf da ke Kudancin Kaduna.

“Don Allah ku daina bai wa waɗannan mutane (masu garkuwa) kuɗi, wannan shi ne babban ƙalubalen da muke fuskanta,” in ji Ribadu.

“Da yawa daga cikin iyalan waɗannan mutanen sun riga sun biya kuɗin fansa, amma hakan bai sa an sako su ba. Mu ne jami’an tsaro muka kuɓutar da su.”

Ya ƙara da cewa: “Ba kuɗin da ake ba su ne ke kawo sakamakon da ake so ba.

“Waɗannan mutanen, duk lokacin da kuka ba su kuɗi, sai su ƙara inganta aikinsu.

“Ba mu taɓa bai wa kowa ko sisin kwabo ba, kuma ba ma son mutane su ci gaba da yin hakan.”

Ribadu, ya ce ci gaban da aka samu wajen ceto waɗanda aka sace ya samu ne sakamakon jajircewar dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

“Ina matuƙar yaba wa dakarunmu da hukumomin tsaro. Jajircewarsu wajen bin diddigin waɗannan miyagu shi ne dalilin da ya sa muke a nan yau,” in ji Ribadu.

“Saboda jajircewar Shugaban Ƙasa, kullum muna samun ci gaba. Amma sako waɗanda aka kama ba shi ne ƙarshen wannan abu ba.

“Za mu ci gaba da bin diddigin waɗannan ’yan ta’adda har sai sun fuskanci hukunci.”

Mutum 64 da aka ceto sun kwashe sama da wata guda a hannun waɗanda suka sace su.

Daga cikinsu akwai mataimakin darakta a ma’aikatar gwamnati da kuma wani ɗan uwan Bishop Matthew Hassan Kukah na cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato.