✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar N80bn: Kotu ta ba EFCC umarnin tsare Akanta-Janar na Kasa

Ana sa ran EFCC za ta mika Akanta-Janar na Tarayya a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta samu izinin kotu na ci gaba da tsare Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, na tsawon kwanaki.

Wani jami’in EFCC da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewar hukumar ta samu umarnin kotu kan ci gaba da tsare Akanta-Janar.

“Har yanzu yana nan tare da mu, yana ba da hadin kai; za mu samu cikakken bayanin abin da muke nema.

“Abin da ya faru shi ne mun samu umarnin kotu da ya ba mu damar ci gaba da tsare shi har sai mun kammala bincikenmu,” inji majiyar.

Da aka tambaye shi game da lokacin da za a sake shi, jami’in ya ce za a iya gurfanar da Idris a kotu a kowane lokaci,” amma bai ambaci sunan kotun da ta bayar da umarnin ba.

Ya kara da cewa za a iya kwace wasu kadarorin masu alaka da shi a Abuja da Legas da kuma Kano zuwa wani lokaci, inda ya ce hukumar za ta kuma matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba kan kwace su na dindindin matukar an same shi da laifi.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Laraba Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da Akanta-Janar din, bayan EFCC ta tsare shi bisa zargin sama da fadi da kudi Naira biliyan 80 na wasu kwangiloli.

A wata sanarwa da ta aike wa Idris, Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta gargade shi da kada ya je ofis a kowane lokaci.

A cewarta, dakatarwar da aka yi mishi ta yi daidai da ka’idojin aikin gwamnati.

“Bayan tsare ka da EFCC ta yi kwanan nan kan zargin karkatar da kudade, in sanar da dakatar da kai daga aiki ba tare da biyan ka albashi ba daga ranar 18 ga Mayu, 2022,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ci tura, bai amsa wayar kiran wayar da wakilinmu ya yi mishi ba.