Babbar Kotun Abuja ta bayar da belin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babchir Dabid Lawal bayan ya kwana a tsare a hannun Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC). Hukumar ce ta kama Babachir Lawal ta gurfanar da shi a gaban kotu a Talatar da ta gabata, inda bayan fara sauraren karar sai kotun ta ba da umarnin hukumar ta EFCC ta tsare shi zuwa shekaranjiya Laraba.
An gurfanar da tsohon Sakataren Gwamnatin ne a gaban Babbar Kotun Abuja da ke Unguwar Maitama, Abuja bisa tuhuma 10 da suka hada da hadin baki da almundahana. Sauran mutanen da aka gurfanar tare da shi sun hada da Hamidu Dabid Lawal da Suleiman Abubakar da Apeh John Monday da kamfanoni biyu, Rholabision Engineering Ltd. da Josmon Technologies Ltd.
Laifin da ake tuhumarsu da shi ya ta’allaka ne kan almundahana game da kwangilar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayar ta Naira miliyan 544 da aka ba Kamfanin Rholabision Engineering Ltd, ta hannun Kwamitin Shugaban Kasa kan Farfado da Arewa Maso Gabas, domin yanke ciyawa da sauransu.
Wadanda ake tuhuma sun musanta aikata laifin, inda lauya mai shigar da kara, Mohammed Abubakar ya nemi kotu ta sanya ranar da za a fara sauraren shari’ar.
A bangaren lauyan Babachir Lawal, tsohon Ministan Shari’a Akin Olujinmi (SAN) ya bukaci kotun ta saurari batun takardar bukatar belin wadanda yake karewa a kotun.
“Lokacin da na yi yunkurin mika takardar bukatar belin ga masu gabatar da kara na samu cikas, inda suka ki amincewa su amshi takardar bukatar belin. Da safiyar yau (Talata), na sanar wa mai shigar da kara batun, wanda ya shaida mini cewa ba ya da masaniyar cewa wani mutum ya ki amsar takardar bukatar belin. Duk da haka ya nuna cewa a shirye yake ya amshi wannan takarda ta bukatar beli. Don haka ya wajaba a gare ni a yanzu in nuna bukatar belin wadanda ake tuhuma da bakina,” inji Olujinmi.
A lokacin da yake ambatar bukatar belin, ya dogara da wata shari’a da Kotun Daukaka Kara ta yanke, tsakanin marigayi Abiola da Gwamnatin Najeriya, cewa kotu za ta iya amfani da bukatar beli da aka gabatar wa kotu da baki, ba a rubuce ba. Don haka sai ya bukaci kotun ta bayar da belin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar bisa ga sanayya.
Sauran lauyoyin wadanda ake tuhuma tare da Babachir Lawal, sun nemi kotun ta ba da belinsu.
Sai dai kuma lauyan masu shigar da kara ya kalubalanci batun belin, ya nuna rashin amincewa a ba da belin wadanda ake tuhumar. Ya bayyana wa kotu cewa, shari’ar Abiola da Gwamnatin Najeriya da lauyan wanda ake tuhuma ya gindaya a matsayin madogara, ba ta da hurumi a wannan shari’ar ta yanzu. Don haka ya ce, ya zama ka’ida ga lauyan wadanda ake tuhuma ya gabatar da takardar bukatar beli a rubuce. Ya bayyana sashi na 162 na Dokar Gudanar da Shari’ar Masu Laifi (ACJA) a matsayin hujja.
Bayan saurarar dukan batutuwan daga bangarorin ne alkalin kotun, Mai shari’a Jude Okeke ya dage shari’ar zuwa shekaranjiya Laraba, inda kuma a zaman kotun na ranar ya yanke hukuncin amincewa da bayar da beli ga Mista Babachir Lawal da sauran wadanda ake tuhuma tare da shi.