✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wani dan Kudancin Kaduna da zai sake zaben El-Rufa’i – Mikaiah Tokwak

Tsohon Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Kaduna, Honorabul Mikaiah Tokwak ya ce babu wani dan Kudancin Kaduna da zai sake zaben Gwamna Nasiru El-Rufa’i tun…

Tsohon Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Kaduna, Honorabul Mikaiah Tokwak ya ce babu wani dan Kudancin Kaduna da zai sake zaben Gwamna Nasiru El-Rufa’i tun daga matakin jam’iyya a zaben fid da gwani har zuwa zaben gama-gari da za a gudanar a shekarar 2019.

Mikaiah Tokwak, ya bayyana haka ne a wajen wani taron wayar da kan mata da matasa kan harkar siyasa ranar Alhamis da ta gabata a garin kwoi da ke karamar Hukumar Jaba, inda ya ce Gwamna El-Rufa’i ya zama Gwamanan Kaduna ne sakamakon kuri’un mutanen Kudancin Kaduna. “Mutanen Kudanci ne suka ba shi kashi 75 na kuri’ar da ya samu. Amma abin takaici yanzu yana cewa ba mu wuce kashi talatin ba a jihar, har ma yana bugun kirjin cewa ba ya bukatar kuri’unmu. To ina amfanin zaben mutumin da ya ce ba ya bukatar kuri’arka?” in ji shi.

A lokacin da take bayyana makasudin shirya taron, Honorabul Larai Ishaku ta ce saboda irin gudummawar da mata da matasa ke bayarwa a fagen siyasa da kuma muhimmancin da suke da shi, ya sa suka shirya musu wannan bitar don wayar da kansu kan muhimmancin mallakar katin zabe. Da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SOKAPU), bangaren matasa, Kwamred Nasiru Jagaba ya kalubalanci mata da matasa da kada su bari a yi amfani da su a zabuka.