✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wanda zai sake cire sama da N20,000 a rana daya a POS – CBN

Sabon tsarin ya nuna idan kuwa ta POS ne, dubu N20 kacal za a iya cirewa a rana.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya takaita yawan kudin da mutum zai iya cirewa na’urar POS a rana daya zuwa N20,000, a banki kuma ba za su wuce N100,000 ba a mako guda.

Hakan da daya daga cikin irin matakan da babban bankin ya ce zai fito da su domin takaita yawon tsabar kudi a hannun mutane.

Ana sa ran wannan tsari ya soma aiki ya zuwa ranar tara ga watan Janairu, 2023.

Wannan na zuwa ne a lokacin da CBN ke shirye-shirye sakin sabbin takardun Naira da aka sake wa fasali don fara kashewa daga ranar 15 ga Disamba.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin sanarwar da CBN ya fitar ranar Talata mai dauke da sa hannun Darakta a bankin, Haruna Mustafa.