Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kalubalanci shugabannin jam’iyyarsa ta PDP cewar ba za su iya korarsa daga cikinta ba.
Wike, ya bayyana haka ne a wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
- Juyin mulki: MURIC ta bukaci sojojin Najeriya kada su yi koyi da na Gabon
- ‘Tinubu na maimaita kura-kuran Buhari a fannin tattalin arziki’
Ya ce babu wani jigo daga jam’iyyar da zai iya dakatar da shi ko kuma ya kore shi gaba daya.
“Wa zai kore ni? Kamata ya yi na zama mai kira da a binciki wadannan mutane da suka saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyya, ta yadda jam’iyyar ta goyi bayan karba-karba.
“Wa zai dakatar da ni? Babu wanda zai iya wannan kuskuren,” in ji Wike.
Tsohon Gwamnan na Ribas ya ce ya sanar da shugabannin jam’iyyar kafin ya karbi tayin minista daga Shugaban Kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki.
Wike ya kara da cewar har yanzu shi jigo ne a PDP duk da yana aiki da gwamnatin APC.
“Ina so na goyi bayan Asiwaju (Tinubu) ya yi aiki mai kyau,” in ji shi.
Ya kuma ce babu wanda ya nemi uzuri na goyon bayan sauya mulki zuwa kudancin Najeriya.
Wike ya ce, “Muna jiran kwamitin Shugaban Kasa su kammala wa’adinsu, za ku san su wane ne suka yi wa jam’iyyar aiki da kyau.
“Ta yaya wani zai yi magana a kore ni? Jihar da ta kawo Gwamna? Jihar da ta kawo Sanatoci uku? Jihar da ta samar da ’yan majalisar Jiha 32? Jihar da ta samar da 11 daga cikin 13 na ’yan majalisar wakilai.
“Mutumin da zai dakatar da ni shi ne wanda ya gaza samar da Gwamna, wanda ya gaza samar da Sanatoci uku?
“Babu mutumin da zai iya kora ta daga jam’iyyar. Babu wanda zai iya aikata hakan. Don haka batun aikata hakan ma bai taso ba”.