✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wanda cutar Coronavirus za ta kashe a jihata – Ishaku

A ranar Laraba Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da fadi-tashin ganin ba a samu wanda cutar Coronavirus za…

A ranar Laraba Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da fadi-tashin ganin ba a samu wanda cutar Coronavirus za ta kashe ba a jiharsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da mambobin kwamitin yaki da cutar Covid-19 na jihar karkashin jagorancin shugabanta, Dokta Innocent Vakkai, suka gabatar da cikakken bayanin ayyukansu a fadar Gwamnatin da ke Jalingo.

Ya ce gwamnatinsa a halin yanzu tana fadada cibiyar gwaji da wuraren killace masu dauke da kwayoyin cutar domin tabbatar da an bayar kulawa ta musamman wajen yaki da cutar a jihar.

Gwamnan ya kuma shaida wa kwamitin cewa gwagwarmayar da Gwamnatinsa take yi wajen yaki da cutar ya sanya aka samu karancin mutanen da suka kamu da ita kuma babu wanda ta kashe har kawo yanzu.

Ya kirayi al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa dokokin da muhukuntan lafiya suka shar’anta biyayya don dakile yaduwar cutar.

Sai dai sabanin yadda Gwamnan ya bayyana, alkaluman Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) sun nuna cewa, cutar Covid-19 ta hallaka mutum 6 a Jihar Taraba yayin da kuma ta harbi mutum 95.