Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani shugaba da zai ce zai iya kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a shekara mai zuwa.
Ministan ya yi wannan martani bayan an tambaye shi a wani taron manema labarai cewa ko kalubalen tsaron da ake fuskanta a halin yanzu zai kare kafin Shugaba Buhari ya sauka daga mulki a 2023.
- Hatsarin mota ya yi ajalin Zamfarawa 7 a Osun
- Yadda aka kashe dan Majalisar Dokokin Kaduna a hanyar Zariya
Lai Mohammed ya ce ba ya tsammani ko shugaba Buhari ba shi da tabbacin cewar za a iya murkushe ayyukan ’yan bindiga a shekara mai zuwa.
Ministan ya musanta zargin da ake wa Shugaba Buhari na rashin katabus wajen kare rayukan al’umma da ake kashewa kusan kullum.
Idan ba a manta ba, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Buhari ya yi iya kokarinsa, babu wani abin da zai iya tabukawa fiye da hakan a nan gaba.
Matsalar tsaro da ta yi kamari musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda ta sa mutane da dama fusata har aka shiga yi wa Shugaba Buhari zanga-zanga, don kawo karshen zubar da jinin al’umma da ake yi a yankin.