Gwamnatin Kano ta ce babu ranar dawo da biyan mafi karancin albashin N30,000 ga ma’aikatan Jihar.
Gwamna Ganduje ya ce duk da cewa gwamnatin jihar ba ta san lokacin da za ta ci gaba da biya sabon mafi karancin albashin na N30,600 ba, ba za ta koma ga tsohon albashin N18,000 ba.
- Azumin Bana: ’Da kyar muke samun abinci’
- Sarkin Musulmi bai halarci jana’izar diyar Sardauna ba
- Tallafin COVID-19: Majalisa ta kalubalanci Minista kan yadda ta kashe N32.4bn
- An mayar da mu saniyar ware a aikin titin jirgin kasa –Gwamnan Gombe
“A shirye muke mu biya albashin N30,600 da muka yi yarjejeniya da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), amma mun yi bayani cewa idan aka samu matsala za mu sake zama da ita mu lalubo mafita,” inji shi.
Ganduje ya kuma roki ma’aikatan jihar da su fahimci irin halin rashin kudade da gwamanti ta tsinci kanta a ciki, wanda ya sa har yanzu ba ta yanke abin da za ta biya na albashin watan Afrilu ba.
Ya yi bayanin ne a ranar Juma’a ta bakin Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Muhammad Garba, a taron Ranar Ma’aikata da aka gudanar a Sakatariyar Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), reshen Jihar.
Amma Shugaban NLC reshen Jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce ba za su amince da dakatar da biyan cikakken albashin ma’aikata ba, har sai ta kawo musu dalilai masu gamsarwa.
Ya ce babu wata doka a Najeriya yanzu ta biyan albashin N18,000, saboda haka ko da za a yi wani ragi, to sai dai ya kasance daga N30,600 da aka sani a jihar.
“Tunda yanzu an samu karancin kudi, to yaushe, kuma ta yaya za a biya mu cikon a nan gaba?
“Maganar albashin watan Afrilu kuma muna kan tattaunawa da su da sauran kungiyoyin ma’aikata, nan gaba za mu bayyana matsayinmu a kai,” inji shi.