Fadar Shugaban Kasa ta ce babu mahalukin da ya isa ya karya gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fadi hakan ne a martaninsa ga masu kurarin ballewa daga Najeriya, irinsu Sunday Igboho da Asari Dokubo.
“Mun yarda da adawa a dimokuradiyya, mutane na da ’yancin tsage wa gwamnati gaskiya amma… Babu wanda ya isa ya karya gwamantin nan domin zababbiya ce a dimokuradiyyance,” inji shi.
Ya bayyana masu kurarin ballewar da cewa tsageru ne da aka dauki nauyinsu, suna yaudarar kansu cewa barazanarsu za ta sa Buhari ya ba da kai bori ya hau.
Igboho mai ikirarin fafutikar kwato ’yancin Yarabawa ya ce yankin Kudu maso Yamma ya ce yankin ya balle daga Najeriya, bisa zargin muhimman albarkatun Najeriya na hannun ’yan Arewa, kuma ana kashe Yarabawa ana mamaye filayensu.
Shi kuma Asari Dokubo ya yi ikirarin kafa ‘Gwamnatin Gargajiya ta Biafra’, wadda ya ce kasarta ta hade wasu yankunan Kudu masu Kudu da kuma Kudu maso Gabas.
Amma a raddin Garba Shehu, yayin hirar da tashar talabijin din Channels ta yi da shi, ya ce babu wata manakisa da za ta iya sa gwamnatin Buhari sauka daga kan mulki.
“Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Gwamnatin Buhari na magance matsaloli masu yawa da ke fuskatar kasar da suka hada da ta tsaro kuma muna samun nasara a bangaren noma, tattalin arziki da kuma yaki da zarmiya —muhimman abubuwan da suka kawo gwamnatin kan mulki.
“Abin takaici ne yadda ’yan adawa ke amfani da wadannan abubuwa, amma ina ba da tabbacin cewa Shugaban Kasa ya dukufa wajen tabbatar kasancewar kasar nan a dunkule.
“Sanin kowa ne cewa kowace kasa tana da matsalolinta, abin bukata daga ’yan kasa nagari shi ne su ba wa gwamnati hadin kwai wajen yakar miyagun laifuka da masu tayar da kayar baya da sauransu.
“Mun yarda da adawa domin dimokuradiyya muke bi, mutane na da ’yancin tsage wa gwamnati gaskiya amma mu yi hattara wurin yin hakan. Babu mahalukin da zai karya gwamantin nan domin zababbiya ce a dimokuradiyyance.
“Gwamnatin dimokuradiyya na kafuwa bayan halastaccen zabe daga lokaci zuwa lokaci, kuma yanzu muna da gwamnati da jam’iyyun siyasa suka mara wa baya ta ci zabe, wannan ya isa shaida cewa har yanzu mutane na tare da ita.”