Sabon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce a tarihin Najeriya, babu gwamnatin da ta taba rayuwar ’yan Najeriya irin ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabinsa jim kadan da ayyana shi a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar na kasa da sanyin safiyar Lahadi.
Aminiya ta rawaito cewa Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon Shugaban ne bayan kammala Babban Taron Jam’iyyar, wanda aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja ranar Asabar.
Ya kuma yaba wa ragowar ’yan takarar da suka janye masa bayan an yi maslaha, inda ya ce su ma nasu babban rabon na tafe nan ba da jimawa ba.
Ya ce, “A madadin sabbin zababbun Shugabannin jam’iyyarmu na kasa, muna mika godiya ga Allah da kuma Shugaban Kasa da Gwamnoni da sauran dukkan mambobin kwamitin riko na kasa saboda aiki tukurun da suka yi wajen samun nasarar taron nan.
“Mun karbi wannan nasarar a matsayin kalubale, kuma za mu iya bakin kokarinmu wajen ganin mun ciyar da wannan jam’iyyar gaba don bunkasar Najeriya.
“Tsawon shekara bakwai ke nan, jam’iyyar APC a matakin tarayya da jihohi da kananan hukumomi, tana aiki ba dare ba rana wajen cire wa ’yan Najeriya kitse a wuta.
“Babu wata gwamnati a tarihin Najeriya da ta aiwatar da muhimman ayyukan da suka shafi rayuwar mutane kai tsaye, musamman wajen manyan ayyuka da inganta rayuwar al’ummar irin ta Buhari.
“Ayyukan da a baya kawai a mafarki ake iya tsinkayo su irin su Gadar Neja ta Biyu da aikin titin Legas zuwa Ibadan da aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna da aikin shimfida bututan iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, dukkansu suna nan ko dai an fara, ko ma an kammala.
“Babu gwamnatin da za ta iya biya wa kowa bukatunsa, komai kokarinta kuwa. Wasu ayyukan dole a tafi ba a kammala su ba, wadanda kuma aka kammala za su bukaci gyare-gyare da ingantawa,” inji Abdullahi Adamu.