✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu gudu babu ja da baya kan Zaben Anambra — INEC

Farfesa Yakubu ya ce INEC ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zabe.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar cewa babu gudu babu ja da baya wajen aiwatar da zaben gwamnan Jihar Abambra a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bai wa al’ummar Jihar Anambra tabbacin cewa ba bu abin da zai hana zaben kamar yadda aka tsara.

Farfesa Yakubu ya ce INEC ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci a duk fadin Kananan Hukumomi 21 da ke jihar.

A wani taron masu ruwa da tsaki na ranar Talata da ya halarta a Babban Ofishin INEC da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra, Farfesa Yakubu ya bukaci jami’an tsaro da su bayar da hadin kai domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana.

Ya ce tuni dai Rundunar yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Babban Sufeton Yan sanda, Usman Baba, ta sha alwashin murkushe duk wani yunkuri da zai kawo wa zaben cikas.

Rahotanni sun bayyana cewa, ita ma kungiyar MASSOB mai fafutikar kafuwar Biyafara, ta ce babu wanda ya isa ya hana gudanar da zaben na ranar Asabar.

Duk dai wannan tabbaci na zuwa ne yayin da a bayan nan kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara ta IPOB ta yi barazanar hana gudanar da zaben.