Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin Jihar Kogi ta yi ba karya doka ba ne.
Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda dalilin da ta ce na tsaro ne.
- Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola
- HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Miller Ɗantawaye, ya ce hana taron ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu cewa za a samu barzanar tsaro, wanda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar matakin.
Sai dai Natasha wadda ta isa jihar a wani jirgi mai saukar ungulu, ta bayyana wa magoya bayanta cewa tana da ’yancin kasancewa da mutanenta ta kuma yi shagalin farin ciki tare da su.
“A duk abin da za mu yi, mu sanya Allah a farko kuma mu shigar masa da buƙatunmu ta hanyar addu’a.
“Mijina ya kasance ɗaya daga cikin addu’o’ina da Allah Ya amsa. In banda haka ta yaya ni da ba kowa ba ce fa ce talaka daga ƙabilar Ebira na samu ƙarfin samun jirgin da zai kawo ni gida?
“Goyon bayan mijina ne ya kawo haka, kuma shi ke ciyar da ni gaba a koda yaushe.
“Tun jiya da na samu labarin za a rufe hanyoyi, aka kuma haramta taruka da jerin gwanon motoci a cikin gari na san cewa mu ne ake so a muzgunawa.
“Amma sai na faɗa wa kaina ai ba kakar siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba ne yanzu.
“Don haka ni ba yaƙin neman zaɓe zan yi ba. Ni kaɗai ce zan shigo gari cikin mutane na, na yi shagalin bikin Sallah tare da su.
“Don haka babu wani laifi a ciki, babu dokar da na karya. A Najeriya muke. Ina da ’yancin shiga taruka da bukukuwa.
Babu gudu babu ja da baya a wannan gangami — Natasha
Aminiya ta ruwaito yadda Sanata Natasha ta mayar wa gwamnati da rundunar yan sandan jihar ta Kogi martanin cewa “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta.
Natasha ta yi martanin ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Ta bayyana cewa “babu gudu babu ja da baya dangane da wannan gangamin na Sallah.
Ta yi zargin cewa duk wani abu da ya faru za ta ɗora alhakinsa ne a kan Gwamna jihar, Ahmed Usman Ododo da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
“Kuma duk abin da ya same mu to za mu ɗora alhakin ne kan gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo, Yahaya Bello da Godswill Akpabio,” a cewar saƙon.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta nemi Sanata Natasha ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a jihar.
Dalilin da muka haramta duk wani gangami a Kogi — ’Yan sanda
Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.
A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.
Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.
“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.
A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.