✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu dan takarar PDP daga Kudu da zai iya kawo karshen matsalar Najeriya’

Kungiyar ta ce babu wata maslaha da aka cimma wajen fitar da dan takara daga arewa.

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa (NYLF), ta ce babu wani daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa daga kudancin kasar nan a PDP da zai iya kawo karshen matsalar da Najeriya ke fuskanta a yanzu.

Kungiyar ta bayyana cewa yankin Arewa bai fitar da wani dan takarar shugaban kasa ta hanyar yin maslaha ba, sabanin matsayin Kungiyar Dattawan Arewa kamar yadda Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana.

Shugaban NYLF na kasa, Elliot Afiyo ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya zanta da manema labarai a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Afiyo ya ce Arewa bai zama lallai ta samar da shugaban kasa a 2023 amma dole ne shugaba mai jiran gado ya kasance shugaba mai kishin kasa don sauya halin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Ya ce jam’iyya mai mulki ta APC ta manta da alkawuran da ta daukar wa talakawa a yayin yakin neman zabenta, wanda hakan ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin halin ni ‘yasu.

“Mun tsinci kanmu a cikin yanayin da ba mu saba gani ba, wanda ke bukatar mafita cikin gaggawa.

“Ba wai muna dagewa cewa dole ne arewa ta fitar da shugaban kasa ba, amma muna bukatar mu sanar da ‘yan Najeriya cewa muna bukatar wanda ya kware, wanda yake da kishin siyasa, wanda zai iya jajircewa wajen kawo sauyi.

“Dole ne irin wannan mutumin ya wanda zai iya sa wa a yi, ya kuma hana an hanu.

“Duk za ku yarda da ni cewa duk masu neman takarar da suka fito daga arewa da kudu, idan na yi ba daidai ba a gyara min amma babu wani daga kudu da zai iya ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki,” in ji Afiyo.

Ya kara da cewa duk da cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mutumin kirki ne, amma ba shi da himmar aiwatar da aiki kan tsarin kundin mulkin kasa na 2014.

Kazalika,  ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji ra’ayin yanki da kabilanci wajen zaben shugaban kasar na gaba.

Afiyo ya yi karin haske kan takaddamar da ake yi kan fitar da dan takara daga arewa ta hanyar yun masalaha, inda ya ce wancan batu ba shi da tushe daga tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babagida ko kuma kungiyar dattawan arewa.

Ya ce, “Ba daidai ba ne a ce Arewa tana da dan takarar shugaban kasa, ba mu da dan takara kuma IBB bai amince da wani dan takara ba.

“IBB dan kasa ne na nagari, ba zai taba yarda ya fifita bukatar kashin kansa fiye da bukatar kasa ba.

“Don haka IBB bai fitar da dan takara ba, kuma Kungiyar Dattawan Arewa ma ba ta fitar da wani dan takara ta hanyar yin maslaha ba.

“Zabin kwamiti ba zabib kungiyar dattawan arewa bane ko zabin IBB.”