✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Babu dan Boko Haram ko daya da ya rage bayan harin Kuje —Ministan Tsaro

Mayaka kusan 300 ne suka kai harin ranar Talata da dare

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce daukacin mayakan Boko Haram sun tsere bayan harin da aka kai a Gidan Yarin Kuje, inda ake tsare da su.

Magashi ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa akalla fursunoni 600 ne suka tsare bayan harin da wasu mayaka kusan 300 suka kai ranar Talata da dare.

“Bisa bayanan da muka samu, mun yi amanna ’yan wata kungiya ne suka kai harin, musamman Boko Haram, saboda akwai ’yan kungiyar da ke tsare a gidan yarin, amma bayan harin ba a ga mutum daya daga cikinsu ba.

“Ina ji mayakan sun kai 64 kuma yanzu babu ko daya daga cikinsu da aka gani a gidan yarin.”

Majiyoyin sun shaida mana cewa akwai manyan kwamandojin Boko Haram da ’yan bindiga da ake tsare da su a Gidan Yarin Kuje gabanin harin na ranar Talata da da dare.

Magashi ya ce “Mayakan sun su ne da yawa suka kutsa ta babbar kofar gidan yarin suka saki fursunoni, wanda yanzu muke aiki domin gano irin fursunonin da suka saki.

“Na gaba za mu ba da aihinin alkaluman wadanda suka tsere, baya ga kokarin da muke yi na cafko su.

“Fursuna kimanin 994 ne a gidan yarin, daga ciki 600 sun tsere, an kama wasu an dawo da su kuma akwai yiwuwar zuwa anjima a sake kamo wasu,” inji minisan.