Jama’ar yankin Batsari na jihar Katsina sun karyata rohoton sojojin Najeriya da ke cewa sojojin sun kashe ‘yan bindiga 46 a garin ‘Yar Gamji.
Kungiyar Cigaban Karamar Hukumar Batsari (BALDF) ta ce babu wani jami’in tsaro da ya tunkari ‘yan bindigar da suka kai wa kauyen ‘Yar Gamji hari suka kuma kashe mutum 18.
“Babu gaskiya a maganar cewa an kashe ‘yan bindiga 46 saboda ba a ma yi fada da su ba”, inji shugaban BALDF Sani Muslim.
Kungiyar ta bayyana haka ne a martaninta ga jawabin Darektan Yada Labarai na Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche da ke cewa dakarun soji na Operation Hadarin Daji sun kashe maharan.
Shugaban kungiyar wanda ya yaba kokarin jami’an tsaro wajen kare al’umma, amma ya bukaci su rika ba wa jama’a sahihan bayanai kan ayyukansu ta hanyar hotuna da bidiyo.
“Ya kamata a kara dagewa musamman wajen tattara bayanan sirri da kai wa ‘yan bindigar da suka jefa rayuwarmu cikin kunci hari a kan lokaci.
“Mun yi alkawari kuma a shirye muke mu taimaka wa sojoji musamman da muhimman bayanai”, inji shi.