Malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya ce sam babu cin naman kare a cikin addinin.
Ya fadi hakan ne a zantawarsa da Aminiya a ranar Alhamis yayin da yake martani kan ɓullar ’yan wata sabuwar akida da suka yanka kare suka raba naman ga dalibansu a Kaduna.
- Cikin kwana 45, kuɗin Abdussamad Rabi’u sun ƙaru da Naira biliyan 820
- Tinubu ya sauke shugaban hukumar tattara haraji, ya nada sabo
Ya ce manzon Allah (S.A.W) ya haramta cin dabbobi da ke farauta irin su kare da sauransu, don haka haramun ne Musulmi ya ci kare.
Sai dai ya ce amma akwai wata mazhaba a yankin Iraki da su kuma makaruhi ne cin kare a wajensu.
Ya ce, “Amma mu a kasar nan, cin naman kare haramun ne domin manzon Allah ya haramta don haka Musulmai a nan kasar ba sa cin naman kare.
“Idan ka kawo sabon abu irin wannan, dole a samu raddi a kai, musamman idan ka danganta shi da hakika ko suna a Musulunci.
“Saboda Musulunci dabbobi hudu ya amince a yi amfani da su wurin al’amuran addini, su ne rakumi, shanu da tumaki sai akuya. Duk sauran dabbobi ko da kuwa halal ne kamar kaza da dawisu ba a yanka su da sunan hadaya.
“Dan haka abin da (mutanen suka aikata) ba Musulunci ba ne kuma yana iya tayar da hankalin al’ummar Musulmai musamman ga mabiya mazhabar maliki da suke ganin haramun ne cin naman kare,” in ji Dokta Gumi.
Malamin ya kuma yi kira ga jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, inda ya ce maimakon haka, su yi wa’azi ga irin mutanen da ke da tunanin kin amincewa da hadisin Annabi a kan kuskure suke.
Sheikh Gumi ya nemi hukumomi da su saka ido sosai akan irin wadannan masu akida musamman idan aka yi la’akari da abin da suka aikata a shekarun baya da har rikici an taba yi da su a kasar nan.
Aminiya ta rawaito yadda wasu fusatattun matasa suka rusa gida da makarantar wani malami da ya yanka kare kuma suka ci tare da dalibansa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Nasarawa da ke Kaduna, inda malamin da daliban nasa ke ikirarin Musulunci bai haramta cin naman karen ba.