✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cikin kwana 45, kuɗin Abdussamad Rabi’u sun ƙaru da Naira biliyan 820

Mujallar Forbes ce ta tabbatar da labarin hakan

Kudin attajirin nan na Najeriya kuma shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdussamad Isyaka Rabi’u, sun karu da Dalar Amurka biliyan 1.2, kwatankwacin Naira biliyan 820 a cikin kwana 45 kacal.

Hakan na zuwa ne a karon farko bayan ya farfado daga faduwar da kudadensa suka yi sakamakon faduwar darajar Naira.

Kudaden nasa sun karu ne da sama da Dala biliyan ɗaya tun bayan da suka ragu zuwa kasa da Dala biliyan 5.2 a watan Yuni.

A cewar mujallar Forbes ta Amurka da ke kididdige abin da manyan attajiran duniya suka mallaka, yanzu haka jimillar abin da Abdussamad ya mallaka ya haura Dala biliyan 6.5.

Kudaden nasa dai sun karu da Dala biliyan 1.2 a kwanan nan, bayan da suka tashi daga Dala biliyan 5.3 din da yake da su a ranar 27 ga watan Yuli, zuwa Dala biliyan 6.5, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Hakan dai ta sa ya ci gaba da rike kambunsa na mutum na biyu da ya fi kudi a Najeriya (bayan Aliko Dangote), kuma na biyar a nahiyar Afirka.

Ana dai alakanta karuwar kudaden na shi da tashin farashin hannun jarin kamfanonin shi na BUA a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

Kamfanonin nasa dai na samar da sukari da man girki da fulawa da taliya da shinkafa sai kuma siminti.

Shi ne dai shugaban kamfanin samar da kayayyakin abinci na BUA, kuma shi ne ya mallaki kaso 92.6 cikin 100 na hannun jarin kamfanonin.