Kamfanonin siminti sun amince su rage farashinsa daga Naira 10,000 zuwa Naira 8,000 ko Naira 7,000 kan kowane buhu matukar Gwamnatin Tarayya ta amince da sharudansu.
An cimma matsayar ne a wani taro da Ministan Ayyuka, David Umahi ya shirya wa kamfanonin.
Umahi ya gayyaci masu kamfanonin siminti wani taro a Abuja bayan da farashin siminti ya tashi zuwa Naira 15,000 a wasu yankunan kasar nan.
Da yake jawabi bayan taron, Doris Uzoka-Anite, daya daga cikin shugabannin kamfanonin siminti, ya bayyana rashin kyawun hanyoyi, tsadar makamashi, da tashin dalar Amurka a matsayin abubuwan da suka haifar da tashin farashin simintin.
“Kamfanonin siminti sun shaida wa gwamnati cewar bai kamata tsadar siminti ta kai yanayin da ake ciki a yau ba. Duk tsadar kilogiram 50 na siminti bai kamata ya wuce Naira 7,000 zuwa 8,000 ba.
“Saboda haka gwamnati da masu kamfanonin siminti da suka hada da Dangote da BUA da Lafarge sun amince a rage farashin siminti daga Naira 7,000 zuwa Naira 8,000, amma tsadar ta danganta da wuraren da za a sayar da siminti.”
A makon da ya gabata ne, siminti ya yi tashin gwauron zabi daga Naira 5,000 zuwa Naira 10,000 da Naira 15,000 a wasu yankuna.
Tattalin arzikin Najeriya ya fada yanayin da bai taba shiga ba a tarihin kasar, lamarin da ya haifar da tashin farashin kayayyaki.