✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Najeriya ne da kansu suke taimaka wa ’yan ta’adda da kudade – Ribadu

Ya ce kudaden su ne babbar hanyar da ’yan ta'addan ke samun kudin shiga

Ofishin mai ba Shugaban Kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce kudaden fansa da mutane suke ba masu garkuwa ita ce babbar hanyar samar wa ’yan ta’adda kudaden shiga.

Ko’odinetan cibiyar yaki da ta’addanci a ofishin, Riya Admiral Yaminu Musa ne ya bayyana hakan yayin wani taron kara wa juna sani da ofishin ya shirya tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Birtaniya.

Yaminu ya ce, “Yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na daya daga cikin manyan hanyoyin samar wa da ’yan ta’adda kudade. A sakamakon haka, yadda ’yan ta’addan ke samun kudaden tafiyar da harkokinsu babbar barazana ce a fadin duniya,” in ji shi.

Shi kuwa Kakakin hukumar tsaro ta DSS, Peter Afunanya, ya zargi ‘yan siyasa da wasu masu kuɗi da cewa su suke rura wutar ta’addancin.

“Sannan akwai koma-baya da ake samu na tarbiyya tun daga tushen iyali. Gida, wanda shi ne matakin tarbiyya yanzu ya tabarbare. Kyawawan dabi’un da aka san mu da su a baya yanzu duk sai bacewa suke yi,” in ji Afunanya.

Kakakin ya kuma ce rundunar ta kafa wani sashe na musamman domin yaki da garkuwa da mutane.

Shi ma Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa, Olumuyiwa Adejobi, cewa ya yi, “Garkuwa ta kaso wurare da dama. Da farko an fara garkuwa domin neman kudin fansa. Daga bisani sai wani sabon salon ya zo ma garkuwa da mutane, a karbi kudin fansa sannan a kashe shi daga bisani.”

%d bloggers like this: