Wanda ya warware wani al’amari da ya kulla da wawa ko mai rauni ko al’mubazzari, ko saboda shugaba bai kasance karkashin tsaro (kulawan) shugaba ba. An karbo daga Jabir Allah ya yarda da shi cewa: Lallai Annabi (S.A.W) ya warware sadakar (mutum matalauci) kafin hanin sa, sa’annan ya hane shi (game da haka).” Malik ya ce, “Idan ya kasance mutum yana da bashin wani mutum akan sa sannan (shi wanda ake bi bashi) yana da bawa sai ya ‘yanta shi to ‘yan tawar ba ta yiwu ba. Haka wanda ya yi ciniki da mai rauni da makamantarsa sai ya bayar da kudinsa gare shi kuma ya umurce shi da gyara wa ko tsayuwa bisa sha’aninsa idan zai barnata shi bayan haka sai ya hana shi. Saboda Annabi (S.A.W) ya hana game da barnar dukiya, kuma ya fadi ga wanda ake yaudara cikin ciniki da ya rika cewa kamar haka: Idan za ka yi ciniki ka ce, “ban da yaudara, amma Annabi (S.A.W) bai karbar masa dukiyarsa ba na cinikin da ya taba yi a baya ba.”
136. An karbo daga Musa danIsma’il ya ce: “Abdul Aziz danMuslim ya ba mu labari ya ce, Abdullahi danDinar ya ba mu labari ya ce, Na ji danUmar Allah ya yarda da su ya ce: “Wani mutum ya kasance ana yaudararsa cikin ciniki, sai Annabi (S.A.W) ya ce masa: Idan za ka yi ciniki ka rika cewa: Ban da yaudara (cuta),” sai ya rika fadin haka.”
137. An karbo daga Asim danAliyu ya ce: “dan Abi Dhi’ab ya ba mu labari daga Muhammad dan Munkadir daga Jabir Allah Ya yarda shi cewa: Lallai wani mutum ya ‘yanta bawansa, kuma bashi da wani dukiya ban da shi, sai Annabi (S.A.W) ya warware hukuncin Nu’aim dan Nahham ya saye shi.”
BABI NA ISHIRIN DA UKU:-
Maganar masu husuma sashensu ga sashe.
138. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abu Mu’awiyat ya ba mu labari daga A’amashi daga Shakik daga Abdullahi Allah Ya yarda da shi ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wanda ya rantse bisa ga wani abin ranstuwa alhali shi a cikin ta fajiri ne don ya amshe dukiyar wani Musulmi da ita, to zai hadu da Allah Yana fushi da shi.” Ya ce, “Sai Ash’ath ya ce, “Wallahi cikin al’amarina wannan magana ta faru, ya kasance tsakanina da wani mutum daga Yahudawa muna husuma akan wata kasa ya rika jayayya da ni, sai na gabatar da shi zuwa ga Annabi (S.AW) sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce mini shin kana da shaida (hujja)? Na ce, “A’a,” sai ya ce wa Bayahude, “Kai rantse,” ya ce, na ce, “Ya Manzon Allah! Idan ya rantse ya tafi da dukiya ta.” Sai Allah Madaukaki Ya saukar da cewa: “Lallai wadanda ke sayen alkawarin Allah da rantsuwoyinsu bisa ‘yan tamanni (kudi) kadan..har zuwa karshen aya (3:77).”