✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babbar Kasuwar Jos mallakar Gwamnatin Filato ce —Lalong

Gwamna Lalong ya gargadi ’yan siyasar jihar da su guji korar masu son zuba jari a Jihar Filato.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana cewa Babbar Kasuwar Jos da ta kone kuma ake kokarin sake ginawa, ta gwamnatin jihar ce ba ta Bankin Jaiz ba.

Lalong ya kuma bayyana cewa kasuwar za ta ci gaba da kasancewa ta gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake aza harsashin ginin wasu rukunin gidaje, da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Odigbo Properties Ltd, zai gina a Dweidu da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a jihar.

Ya ce “bari na gaya maku gaskiyar magana kan cece-kucen da ake yi kan maganar sake gina Babbar Kasuwar Jos da ake cewa gwamnatin Filato ta cefanar wa Bankin Jaiz.

“Wannan kasuwa mallakar gwamnatin Filato ce, wadda hukumar kasuwar da ke karkashin gwamnatin Filato ta shafe shekara 40 tana kula da ita.

“Saboda haka za ta ci gaba da kasancewa mallakar gwamnatin Filato duk da cewa mutane za su iya sayen shaguna a wannan kasuwa.

“Don haka, ina kira ga al’ummar jihar nan, su yi watsi da masu farfagandar cewa, za a sayar da wannan kasuwa ga bankin musulunci.”

Gwamna Lalong ya kuma gargadi ’yan siyasar jihar da su  guji korar ’yan kasuwa masu son zuwa jihar zuba jari ta hanyar yada wannan jita-jita.

Ya ce sam bai da ce ba, a rika yada irin wannan farfaganda ta siyasa kan abubuwan da za su kawo wa jihar ci gaba.

“Babu shakka irin wannan farfaganda za ta hana bakin ’yan kasuwa masu zuba jari shigowa jihar su zuba kudadensu.

Gwamna Lalong ya yaba wa kamfanin Odigbo Properties kan yadda ya zabi gina gidaje musamman a wannan lokaci da ake matukar bukatar muhalli a jihar.

Da yake jawabi, Shugaban kamfanin na Odigbo Properties, Mista Chikezie Tony, ya bayyana cewa kamfanin ya zabi aiwatar da wannan aiki ne saboda zaman lafiyar da aka samu a jihar.

Ya ce wadannan kananan gidaje guda 300 masu yawan dakuna daban-daban kuma masu inganci da za su gina, za su sayar da su kan farashi mai rahusa.