✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babban taro: Rikici ya yi awon gaba da kujerar shugaban kungiyar Gwamnonin APC

Lamarin na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke fama da rikici a kan babban taronta da ke tafe.

Yayin da rikici kan lokacin gudanar da babban taron jam’iyyar APC mai mulki ke dada kamari, Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar, Salihu Mohammed Lukman, ya ajiye mukaminsa.

Wakilinmu ya rawaito cewa Salihu ya ajiye mukamin nasa ne ranar Litinin bayan wata gagarumar baraka da aka samu tsakanin Gwamnonin jam’iyyar a tsaron da suka yi da maraicen ranar Lahadi a Abuja.

Wata majiya da ke da kusanci da Darakta Janar din wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce tuni ya mika takardar ajiye mukamin ga Shugaban Kungiyar, kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu.

Kazalika, majiyar ta tsegunta wa wakilin namu cewa wasu Gwamnoni ne suka bukaci ko dai ya sauka daga mukamin ko kuma a tsige shi yayi taron nasu.

Bayanai sun nuna cewa ko da yake akasarin Gwamnonin sun bukaci a kyale shi, amma wasu sun tsaya kai da fata kan sai ya tafi.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, wayoyin Salihun sun kasance a kashe lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa.

A ’yan kwanakin nan dai ya sha cakaki a kan wasu batutuwan da suka shafi jam’iyyar, wanda suke kallon yana yi mata zagon kasa.