Shugaban Hukumar Koyar da Sana’o’i ta kasa (NDE), Dokta Nasiru Mohammed ya bayyana cewa babban buri ko manufar hukumarsa ita ce koyar da mutane sana’a da kuma horar da su.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyararci babban ofishin kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya a Abuja tare da tawagarsa.
Dokta Mohammed ya ce suna da ofishi a duk lungu da sakon kasar nan, sannan kuma suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun taba rayuwar al’umma, wanda hakan ya sa suke neman hadin gwiwa da kafafen watsa labarai domin cin ma burinsu.
“Da muna da ayyuka kusan 74, amma da na fara aiki sai na rage su suka dawo guda 17 bayan mun duba kuma mun gano wadanda aka fi bukata.
“A bangaren tallafa wa mutanen karkara kuwa, muna kokari matuka wajen koyar da mutane harkokin noma. Haka kuma a yankin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya dabaibaye na shekaru, mun kammala shirye-shiryen koya wa mata da matasa sana’o’i a jihohin yankin, wanda yanzu haka muna kokarin samun hadin gwiwar Gwamnan Jihar Borno domin a jiharsa ne za gudanar da shirin.
“Su ma wadanda suka dawo daga Libya, mun je Jihar Edo inda muka tattauna da Gwamnan Jihar a kan yadda za mu taimaka masu. Bayan mun gana da su wadanda suka dawo din, mun gane cewa yawancinsu suna da sana’a, don haka sai muka ce za mu rika daukarsu a matsayin masu horar da mutane.”
Shugaban hukumar ya kara da cewa suna bayar da jari, duk da cewa suna fama da matsala wajen dawo da bashin. “Muna samun matsala da mutane wajen biyan bashin da suka karba. Abin da na yi bayan na fara aiki shi ne, ya fito da tsarin karfafa wa bangaren bibiyar bashin da muka bayar, sannan kuma muka ce za mu ba su wani kaso daga cikin kudin da suka karbo.”
Daga karshe sai shugaban ya yi godiya ga kamfanin Media Trust bisa yadda aka tarbe su.